Dalilin da ya sa nake horar da kwallon kafa a Najeriya —Koci Dobreb

Mitko Dobreb mai kimanin shekara 61, dan kasar Bulgeriya, shi ne kocin kulob din IfeanyiUba da ke Jihar Anambra, a hirarsa da Aminiya a kwanakin baya lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da kulob din Giwa FC a Jos, ya bayyana dalilin da ya sa ya zo Najeriya da nasarorin da ya samu da […]

Dalilin da ya sa nake horar da kwallon kafa a Najeriya —Koci Dobreb
Dalilin da ya sa nake horar da kwallon kafa a Najeriya —Koci Dobreb

Mitko Dobreb mai kimanin shekara 61, dan kasar Bulgeriya, shi ne kocin kulob din IfeanyiUba da ke Jihar Anambra, a hirarsa da Aminiya a kwanakin baya lokacin da kulob dinsa ya buga wasa da kulob din Giwa FC a Jos, ya bayyana dalilin da ya sa ya zo Najeriya da nasarorin da ya samu da kuma yadda yake hango kulob dinsa a nan gaba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Za mu fara da gabatar da kanka

Sunana Mitko Dobreb, an haife ni a ranar 26 ga Fabrairu, 1954 a yankin Kudancin kasar Bulgeriya da ake kira Haskobo. Na shafe fiye da shekara 35 ina harkar kwallon kafa.

Me ya ja hankalinka har ka zo Afirka musamman ma Najeriya don koyar da harkar kwallo?
Ina son Afirka, don haka ban yarda in tsaya a son Afirka a fatar baki ba, na fada wa kaina idan kana son Afirka ya kamata ka bada gudunmuwarka wajen bunkasa nahiyar, to ni abin da na fi kwarewa shi ne harkar kwallon kafa, don haka sai na zo Afirka don bunkasa harkar kwallon kafa, inda na koyar da kwallon kafa a Najeriya da kuma Ghana, yanzu kuma na sake dawowa Najeriya.

Me ya dawo da kai Najeriya bayan ka yi aiki da kulob din Heartland daga 2007 zuwa 2009, inda rahoto ya bayyana ba ku yi rabuwar arziki ba?
A yanzu tattalin arzikin kasarmu ya samu kansa cikin mawuyacin hali, don haka ba shi da karfin da zai rike harkar kwallo a kasar, wannan dalili ya sa na yanke shawarar in dawo Najeriya don bunkasa harkar kwallon kafa, kasancewar duk da halin da tattalin arzikin Najeriya ya samu kansa a ciki, to gara shi da na kasarmu, wanda a yanzu ga ni ina horar da ’yan wasan kulob din IfeanyiUba da ke garin Nnewi a Jihar Anambra.

Me ya sa ba ka zabi aiki da manyan kulob-kulob na Najeriya kamar Kano Pillars da Enyimba FC ko Warri Wolbes ba, sai ka zabi FC IfeanyiUba wanda a bana suka dawo buga gasar Premier ta Najeriya?
Idan kana so a tabbatar da aikinka a matsayinka na mai horarwa, to ka samu kulob din da ba a masa zaton taka rawar a zo a gani, sai ka mayar da shi wani abu, hakan zai ba ka daraja, don haka a lokacin da shugabannin wannan kulob suka tuntube ni ban yi kasa a gwiwa ba, duk da cewa a lokacin ina horar da kulob din Heart of Oaks da ke Accra babban birnin kasar Ghana ne, kuma mu ne muka lashe gasar Premier ta kasar.

Wadanne nasarori ka cim ma zuwa yanzu?
Na fara harkar kwallon kafa sosai a shekarar 1982, inda tsakanin 1982 zuwa 1995 na rike kulob hudu da suka hada da FC Dimitrobgrad da FC Hebros Harmanli da FC Boteb-Simeonobgrad da kuma FC Marsa-Haskobo. Daga 1995 zuwa 1998 na zama babban mai horar da kulob din FC Hoskoba. Daga 1998 zuwa 1999 kuma ni ne Babban Daraktan kulob din FC Olympic-Teteben na kasar Bulgeriya, sannan daga 1999 zuwa 2002 na zama babban mai horar da ’yan wasa kulob din FC Toplica-Mineralni Bani da ke Haskobo, sannan aka zabe ni shugaban hukumar ’yan wasan cikin gida a Jamhuriya Bulgeriya.
Daga shekarar 2002 zuwa 2005 na rike kulob din FC Sbilengrad. Na lashe kofin kakar gasar Premier na kasar Ghana ta shekarar 2006/2007 da kulob din Hearts of Oak. A shekarar 2007 aka zabi ne cikin gwarazan koci uku na kasar Ghana. A 2007 na lashe kofin kalubale na Jihar Imo. Daga nan na zama kocin kulob din Heartland a Najeriya daga 2007 zuwa 2009, inda a tsakanin wadannan shekaru kulob ya gama a matsayi na biyu a gasar premier.
A bana kulob din IfeanyiUba ya lashe kofin Super Four da aka yi a watan Fabrairu, bayan mun doke kulob din Shooting Star da ci 2-0.

Yaya kake magana da ’yan wasa kasancewar kasarka ba Turanci ake yi ba?
Ina jin yaren Ingilishi da na Rasha da kuma wadansu yaruka na Bulgeriya. Kuma ka san Najeriya da Ghana duka yaren Ingilishi ake yi, don haka ba na samun wata matsala wajen magana da ’yan wasana.

Yaya kake hasashen kulob din FC IfeanyiUba a nan gaba?
Ina hasashen nan da shekara uku ’yan wasan wannan kulob din za su cika kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles). Ka ga kocin Najeriya ya gayyaci golanmu Chidiebere Eze a lokacin da Super Eagles ta buga wasan sada zumunci da kasar Uganda da kuma Afirka ta Kudu, bayan Eze muna da zakakuran ’yan wasa kamar su Chiburzor Okonkwo da Adeleke da sauransu da nan gaba kadan za a ga fitilarsu na haskakawa.

Wane kalubale kake fuskanta a kulob din FC IfeanyiUba?
Ba ni da wata matsala, domin muna da isasshen kudi, muna taka leda a sabon filin wasa, sannan kamfanin da ke daukar nauyinmu mai suna Capital Oil yana samar mana da duk wani abu da muke bukata, ya saya mana sababbin motoci, ya samar mana da kayayyakin atisaye da sauransu, sannan ’yan wasana suna bin umarnin da na ba su yayin atisaye da kuma wasa, don haka nan gaba kadan idan ba mu zo na daya a Najeriya ba, to ba za mu wuce na biyu ba.

Mene ne burinka a wannan kulob din?
Za mu dauko manyan ’yan wasa uku, kada ka manta dukkan yarana suna atisaye ba-ji-ba-gani, don haka burina in samar mana da tikitin buga gasar zakarun Afirka, sannan in lashe kofin kalubale na bana.

An zarge ka da yi wa kulob din Heartland zagon kasa da kuma nuna miyagun halaye a lokacin da kake kulob din, wanda haka ya sanya kulob din ya sallame ka, ko me za ka ce kan haka?
Wannan wani al’amari ne da ya faru a baya, wanda a yanzu tuni na manta da shi, a yanzu ba ni da wani abu da yake gabana face daukaka martabar kulob din FC IfeanyiUba. Kada ka manta a lokacin da zan dawo Najeriya karo na biyu kulob din Heartland na daya daga cikin kulob-kulob din na so yin aiki da su, amma a karshe saboda dalilin na bayyana maka a baya, sai na zabi FC IfeanyiUba, sannan kada ka manta manyan koci-koci na duniya ma sun bar kulob bayan samun sabani, sannan suka sake dawowa, misali, Jose Mourinho ya bar Chelsea bayan sabanin da ya samu da mai kulob din Roman Abromabich, inda kuma sake dawowa, sannan Neil Wannock ya bar Crystal Palace da ke Ingila, sannan ya sake komawa, don haka ba ni da wata matsala da kulob din Heartland.

Me za ka ce dangane da mutanen Najeriya?
Ina son al’adun kasashen Afirka musamman ma Najeriya, mutanen Najeriya suna daraja baki, ina jin dadin yadda suke martaba ni, hakan ne ma ya sa na sake dawowa Najeriya.

Me za ka ce dangane da harkar kwallon kafa a Najeriya musamman lokacin da kake Heartland a shekarar 2007 da kuma a yanzu?
An samu ci gaba sosai, an samu ci gaba a bangaren biyan ’yan wasa, kwantiragi da kuma yadda ake hura wasa. A lokacin da nake Heartland babu yadda za ka samu nasara idan ba a gida ba, duk yadda ka kai da buga wasa dole sai an samu nasara a kanka, ko ka yi kunnen-doki. Amma yanzu abin ya canza za ka je waje ka samu gagarumar nasara, misali mun ci Elkanemi Warriors 4-1 a gidansu, sannan an ci kwallaye 74 a kakar gasar bana a waje, ka ga abubuwa sun yi kyau.

Sojoji sun daƙile harin Boko Haram, sun ceto mutum 9 a Borno

’Yan sanda sun kashe ’yan fashi 3 a Binuwai

Mahara sun sace bsarake, sun harbi matarsa a ƙauyen Ondo

Sarkin Musulmi ya umarci a fara neman jinjirin watan Muharram