Dalilin da ya sa nake kwanciya a kabari kullum – Dan Malam
Ko za ka yi mana bayanin dalilinka na tona kabari kana shiga lokaci-lokaci a kofar dakinka? Gaskiya duniya ce ta zama wani iri, rashin tsoron Allah ya zama ruwan dare a tsakanin jama’a, son zuciya ma ya zama ruwan dare. Dama Annabi (SAW) ya ce a karshen duniya son zuciya zai yawaita. Ka duba yanzu […]

Ko za ka yi mana bayanin dalilinka na tona kabari kana shiga lokaci-lokaci a kofar dakinka?
Gaskiya duniya ce ta zama wani iri, rashin tsoron Allah ya zama ruwan dare a tsakanin jama’a, son zuciya ma ya zama ruwan dare. Dama Annabi (SAW) ya ce a karshen duniya son zuciya zai yawaita. Ka duba yanzu yadda mutane suka lalace, a ce wai har ta kai mutum zai mutu, a je makabarta domin yi masa biso amma ana aikin bison a yi wa mutane satar waya. Ana sata a Harami (na Makka), ana sata a gidan gobara. Allah Ya ce kada a taba kayan mutum, kada a taba hakkin mutum amma ana yi a wannan zamani. Sata ce, gulma ce duk dai (ga su nan). Kai da mahaifnka a hada ku, mutane da mutane, a hada ku, rashin tsoron Allah ya zama ruwan dare ga zalunci da mugunta. Bisa haka ne na yanke shawara a kashin kaina na ga babu abin da ya kamata in yi domin in tsorata kaina illa in tona kabari a cikin gidanmu, kuma a hurumina ina shiga. Wannan abin yana saka ni in ji tsoron laifuffukana, ba wai don in tsoratar da wani ba. Ina kuma shiga ne lokaci bayan lokaci domin in tuna wa kaina da yadda na kasance a duniya, da yadda za a bisne ni bayan na mutu.
Me ya ba ka sha’awar shiga cikin kabari?
Gaskiya idan na shiga na fito gaskiya ina gyara wasu laifuffukana sosai, don haka nake jin dadi sosai. Sannan idan na zo fita daga cikin gidana, nakan dauka idan na dawo kawai za a kawo ni cikin kabarin nan ne. Wannan shi ne abin da nake sanyawa a cikin raina, ina ganin kamar za a kawo ni a matsayin matacce ne, tunda Allah bai ce ga lokacin da zan mutu ba, amma dai na san kowane rai mamaci ne. Don haka sai nake ganin idan na fita to ni gawa ce kawai, don haka bari in yi kokari in rage wasu abubuwan da zan yi wadanda za su taba min mutuncina, ko su taba wa iyalina mutunci ko su bata wa wani rai. Don haka sai nake taka-tsantsan da rayuwa a lokacin da na fita harkokina na yau da kullum. Idan zan fita sai in shiga cikin kabarin, idan na dawo kafin in yi komai sai in shiga domin in rika tunawa da lahirata. Kamar yadda na fada maka ina saka abubuwa da dama a lokacin da na shiga cikin kabarin nawa da na gina domin wa’azantar da kaina.
Akwai abin da ke faruwa da kai in ka shiga kabarin?
Ni dai ina shiga ne lokaci bayan lokaci, ina kuma bari ne sai dare ya shiga tsakiya irin karfe biyun dare zuwa uku haka sai in shiga in kwanta a ciki. Idan na shiga cikin kabarin nakan kwanta ne sai in rika surantawa a raina kamar na mutu ne ina cikin kabari.
Sai in ce yanzu gani na mutu an kawo ni kabari na aikata abubuwa da dama a rayuwata amma ban gyara ba, na yi kaza na yi kaza, to yanzu ga Mala’ika zai zo ya same ni, ta yaya zan yi in gyara wadannan abubuwa da na aikata a duniya? Ina cikin haka sai firgigi in farka in tashi daga cikin kabarin. Sai in ce bari in yi kokarin in je in gyara abubuwan da na aikata na zunubai, na cuci wannan na yi fada da wancan, na bata wa iyayena rai, ko na yi wani abu kaza marar kyau, ko ba na zaune da makwabtana lafiya, duk sai in je in yi gyara. To ka ji yadda nake yi, kuma ina tsoratar da kaina sosai. Idan wannan abin da nake yin zai sanya wani ya ji tsoron Allah, to ban hana shi ya yi koyi da ni ba, ina kuma lale da duk wanda ya ga zai bi ni wajen yin wannan lamarin domin tuba ga mahallici tuba kuma mai kyau. Sannan ina kuma shiga lokacin da zan fita daga gida da kuma lokacin da na dawo.
Ko akwai darasin da kake so jama’a su koya daga wannan aiki naka?
Lallai ina son mutane su rika wa’azantuwa, suna tunawa da makomarsu ta gobe. Ina son su sanya a ransu cewa shi Allah Mai gafara ne, kada ka ji wai don ka yi laifi Allah ba zai yafe maka ba, a’a duk laifuffukanka Allah sai Ya yafe maka idan Ya so matukar za ka roke shi. Akwai wanda ya fi kowa laifi Alkur’ani ya kawo shi, amma da ya tuba ai Allah Ya yafe masa. AllahYa yafe masa ne sakamakon tuban da ya yi, tuba kuma tsakaninsa da Allah irin tubar da Allah yake so. Kuma hikimar tona wannan kabari dai ita ce domin ni da kai da sauran jama’a mu wa’azantu mu gyara halinmu. Kai har da kai da kake min wannan tambayoyin. Kowa ya zama bawan Allah, kada ka cutar da wani, kada ka taba kayan wani, kada ka yi gaba da makwabcinka, duk mutumin da Allah Ya hada ka da shi ka yi zama da shi lafiya. Sannan ina son kowa ya ji tsoron Allah Ya zauna da iyayensa lafiya, kuma ya zama mai gaskiya da adalci a tsakanin jama’a.
Idan aka ce kabari ko makabarta mutane sukan ji tsoro da firgici a ransu, yaya ka jure kake shiga a tsakiyar dare?
Ai babu abin da nake tsoro a duniyar nan irin kabari dalilin da ya sanya na gina shi ke nan domin yana zaburar da ni in ji tsoron akwai ranar da zan hadu da Mahaliccina. Ina shiga ne domin in yi bitar makomata ta gobe. Ina jin tsoro mana, ai tsoron ne ya sa na gina.
Me mutane suke ce maka?
Eh, gaskiya a lokacin da na gina kabari ina shiga wadansu har dariya suke yi min. Akwai wadansu mutum 19 da dariya suke yi min sosai. Yau shekara biyar zuwa bakwai ke nan da na fara wannan suna yi min dariya, a wasu lokatan ma ce min suke yi na yi hauka. Me ya sa zan je in shiga kabari alhali da raina. Yaya ba zan dauki wata hanyar tsoratar da kaina ta daban ba? Yau su da suke ganin suna da hankalin dukansu sun shiga kabari, ni kuma da ba ni da hankalin Allah Ya bar ni. Ka ga wannan wani abu ne da Allah Ya so. Don haka duk mutumin da kabari bai sanya shi ya ji tsoron Allah ba, to gaskiya zai yi matukar wahala imaninsa ya dawo. Saboda haka akwai mutumin da ya yi ayyukan assha fiye da kima, amma da ya nemi tuba an yafe masa. Abin da Allah ba zai yafe maka ba, shi ne shirka, shirkar ma sai ka mutu kana aikatawa ne kafin Allah Ya azabta ka a kanta. Don haka shi Allah Gafurun Rahimun ne.
Ko kana da sha’awar in ka mutu a bisne ka cikin kabarin da ka tona?
A’a, ba a nan za a bisne ni ba, makabartar da ake bisne mutane a nan za a bisne ni. Wannan dai na gina ne kawai domin in tsoratar da kaina. Mutanen da suka tabbatar da wannan abin da nake yi ya gamshe su na yarda su yi koyi su kuma ji tsoron Allah.
Wani sako kake da shi ga jama’a?
Sakona mu ji tsoron Allah, mu kadaita Allah Shi kadai, mu kuma bai wa kowa hakkinsa na zamantakewa da sauransu. Kuma ina kira ga matasa ’yan’uwana su daina aikata assha domin sune manyan gobe.