Dalilin da ya sa wasu mata ba sa samun miji da wuri

Ya ke ‘yar uwa, shin har yanzu kin ga ba ki samu miji ba ko?  Na san idan aka tambaye ki cewa za ki yi ai Allah ne bai Yi ba, ko ki ce ai lokaci ne bai zo ba.(Hmmm) lallai haka zancen yake, amma kin san komai, sai da dalili kuma na san dalilinki, […]

Dalilin da ya sa wasu mata ba sa samun miji da wuri
Dalilin da ya sa wasu mata ba sa samun miji da wuri

Ya ke ‘yar uwa, shin har yanzu kin ga ba ki samu miji ba ko?  Na san idan aka tambaye ki cewa za ki yi ai Allah ne bai Yi ba, ko ki ce ai lokaci ne bai zo ba.
(Hmmm) lallai haka zancen yake, amma kin san komai, sai da dalili kuma na san dalilinki, kuma na san za ki iya tambayar mene ne dalilin?   
 Kai tsaye zan gaya miki dalilin da ya sa ba ki samu miji ba, kuma dalilin shi ne, ki sani dai mu maza tsoronki muke ji kamar yadda muke tsoron mutuwarmu. To, ko kin san me ya kawo haka? Anan ma kar ki damu, kuma kar ki yi garaje ko gajan hakuri domin yanzun nan zan fada miki, don haka ki bude kunnuwanki da kyau ki saurara ki ji.
To, dalili na daya daga cikin dalilan dai shi ne, ‘yar budurwa ta yaya  za ki samu miji alhali kina wulakanta maza da nuna musu izza da isa, kullum idan yamma ta yi idan za ki fita  sai kin dau wanka, kin yi kwalliya  kamar za ki fita gasar sarauniyar kyau. Bayan kin fito daga gidanku za a ga kina tafiya cikin isa da kasaita da ji-ji da kai hadi da izza kina hura hanci, kanki a dage, ke dai ga mace mai aji. To wallahi duk namijin da ya ganki a irin wannan shigar zai zata ke ‘yar wani hamshakin dan kasuwa ce, ko ‘iyar wani baban dan siyasa, idan kuma har ya yi gigin yi miki magana sai ki ki saurararsa, idan ma ya matsa miki sai ki wulakanta shi a bainar jama’a.   To, ke ‘yar uwa saboda Allah ta ina kike tunanin ya-ku-bayina irina ko malami ko dan ustazu mai  karamin karfi  zai iya tunkararki da maganar soyayya wacce ta danganci maganar aure?
Wannan dai shi ne dalilina na daya wanda kuma wannan dalilin zai iya ya hana a tunkare ki da maganar aure ,domin tun farko kin nuna cewa kin fi karfin ajin talaka, alhali ke ma matalauciyar ce diyar talaka.
Idan kuma wani bawan Allah ya yi shahadar kuda ya nemi zuwa wajenki har kika karbi soyayyarsa, daga nan ya fara zuwa wajenki domin yin hira gidanku. Kika fara yin amfani da wannan damar kina  yi masa dariyar yaudara da dare, sai a ga kawai ya fara ramewa tamkar kudin guzuri, daga nan sai a ga ya fara batan wata har zuwa batan sati, har ma ta kai  shi ga batan wata na rashin zuwa wajen ki, idan an yi magana za ki ce ba ki san dalili ba. Amma kuma ni na san dalili, kamar yadda kika boye gaskiya ba ki fada ba, zan tona dalilinsa na rashin zuwa.
Asirin kuwa shi ne, yayin da bawan Allah namiji ya fita domin ya yi ‘yar buga-bugar neman na koko, zafin rana da ruwan sama duk sun sauka a kansa, ke bar ma ta maganar wadannan domin bayansu akwai iska da guguwa da ke bade shi a duk lokacin da suka taso, da kyar da sudin goshi zai samo ‘yan kwabban da ba za su iya  toshe masa wata kafar ba, ke kuma kina gida kwance kina jira ya gama wahalar samowa idan dare ya yi ya zo tadi sai ki tatuke shi  kamar man shafawa.   Bawan Allah, ‘yan kwabban da ya yi gumin kai da na wuya zuwa na goshi har ya tara, kawai cikin mintuna kalilan ko awa daya ba su kai ba sai ki raba shi da su.   Haba ‘yar uwa ta yaya za ki yi tunanin gobe zai yi marmari, ko gigin dawowa wajen ki?  tunda kin mayar da shi tamkar katin cire kudi na ATM ko kuma babban bankin Najeriya, CBN?
Mu dai cigaba da warwara a kan maganar har yanzu ba ki samu mijin ba? To ke ‘yar uwa bar ta wannan ma, ta wace hanya za ki samu miji? alhali namiji ya fito da karfinsa yana so ya aure ki amma ke kuma duk kwanan duniya kina talauta shi da kudin ankon bikin kawayenki, ba a ma batun kudin dinki da kuma  kudin liki, ko kuma za ki bai iwa amarya gudummawa.
Sannan ga mugun kwadayi, kullum sai “darling sayo min abu kaza-da kaza” ko kuma “sayo min shawarma” ko “kaza gasasshiya” alhali ko shi kansa watakila bai taba lasar ko da man kazar ba ballantana shawarma.   Kin hana shi sakat, kullum sai kokari a kan kin karbe masa ‘yan kudin da yake tanadi.   Saboda Allah ‘yar uwa da wane kudin zai aure ki? alhali kina cinye kudin wajen sanya shi yana ban ruwan abin da ba ya tofo ballantana ya yi ‘ya’ya?  To, ba dole ya gaji ya guje ki ba.
Ire-iren wadannan dalilan suna da yawa wadanda suka hana ki samun miji, kike zaune a gida kina gwada tsawo da gogayya da gyatumarki har kina ganin kokon kanta saboda tsawonku  ya zo daya, Idan kuka fito sai a rasa wace ce uwa, wace ce ‘ya daga cikinku?
Haba ‘yar uwa ki sassauta wa rayuwarki ki gane cewa ita fa  rayuwa da sannu ake taka ta.   Ki daure ki yi wa kanki fada da yin kiyamullaili na rashin samun mijin aure. Ki tuna watakila kina da kanne mata, ba za ki so su taso suna jera tsawo da ke ba kamar yadda ke kika gwandare kina gasar nuna tsawo da tsohuwarki.   ‘Yar uwa ki taimaka ki rage kwadayi da buri sai ki ga komai ya zo miki da sauki.
Ya Adon Gari! ina jiran amsarki idan kin fahimci inda na dosa.  Ina so ki yi fushi da ni ki dauki matakin da zai sa ki yi aure nan gaba kadan wanda idan hakan ya faru sai in rasa abin da zan rubuta a kan ki gobe wajen kalubalantarki.

 Wassalamu Alaikum.
Nasir Abbas Babi (Nasaba)
080 63 67 36 56—080 96 96 78 00