Dalilin da ya sa za mu bude jami’ar mata zalla – Sarkin Musulmi

A kokarinta na bai wa karatun mata mahimmanci, musamman karatun zamani, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar lll ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Majalisar Sarkin Musulmi za ta gina jami’ar  na mata zalla a Sakkwato.Sarkin Musulmin ya sanar da haka ne a lokacin wani taro da cibiyarsa ta Sultan Foundation tare da hadin gwiwar […]

Dalilin da ya sa za mu bude jami’ar mata zalla – Sarkin Musulmi
Dalilin da ya sa za mu bude jami’ar mata zalla – Sarkin Musulmi

A kokarinta na bai wa karatun mata mahimmanci, musamman karatun zamani, Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar lll ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba Majalisar Sarkin Musulmi za ta gina jami’ar  na mata zalla a Sakkwato.
Sarkin Musulmin ya sanar da haka ne a lokacin wani taro da cibiyarsa ta Sultan Foundation tare da hadin gwiwar Hukumar kula da jin dadin Yara ta Majalisar  dinkin Duniya (UNICEF) tare kuma da sauran maso ruwa da tsaki a fannin ilimi a jihohin arewacin kasar nan suka shirya a Kaduna a ranar Asabar din da ta gabata.
Sarkin Musulmin ya yi nuni da cewa yanzu zamani ya wuce da iyaye za su rika fifita karatun ‘ya’ya maza a kan na mata domin kuwa mace mai ilimi ta fi wani namijin mai ilimi, don haka akwai bukatar iyaye su canza tunaninsu a kan karatun mata.
Ya kuma nuna damuwarsa a kan yadda ‘yan Nijeriya, musamman a yankin Arewa, wadansu iyayen ba su damu da ilmantar da ‘ya’yansu mata ba, wanda kuma hakan bai dace ba. “ Ilimin mata na da mahimmanci matuka, saboda haka iyaye ya kamata su tabbatar  ‘ya’yansu mata suna karatu, domin a nan Arewa mun san mahimmancin samun likitoci mata a cikin al’ummarmu. Wannan ne ya sa muka ga ya dace nan ba da dadewa ba za mu samar da jami’a na ‘ya’ya mata zalla wanda za a gina a Sakkwato domin amfanin al’ummar Arewa. Tuni na kafa kwamiti da za su tsara mana yadda jami’ar za ta kasance, nan gaba kadan za su kammala aikinsu. Mun yi hakan ne domin nunawa al’ummarmu mahimmancin ilimi. Kuma wannan taron hadin gwiwa da hukumar UNICEF an shirya shi ne domin tattauna taron kasa da za mu yi a Sakkwato a kan mahimmancin karatun ‘ya’ya mata a arewacin kasar nan,” inji shi.
Sultan Abubakar ya ce suna sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci wannan taron da za a yi  a kan bunkasa karatun mata a Arewa.
Sarkin Musulmin ya kuma kara da yin kira ga iyaye da su daina tura ‘ya’yansu bara, domin a cewarsa almajirinci ba musulunci ba ne.
Aminiya ta yi kokarin samun karin bayanin daga Masarautar Sakkwato amma abin ya ci tura, sai ta tuntubi Malam Lawal Maidoki, wanda makusanci ne sosai ga Majalisar Sarkin Musulmi don samun bayani, inda ya ce, “Maganar Jami’ar mata zalla haka ne kuma shirye-shirye sun yi nisa don har an kafa kwamiti karkashin jagorancin Dakta Muhammad Boboye, mambobinsa kuwa sun kunshi Farfesa Fatima Mukhtar da Farfesa Hadiza Galadanci da Dakta Mairo Mandara da Malam Ahamad Makarfi.  An fara Wannan shirin ne a shekarar 2014 karkashin kulawar Sarkin Musulmi. Dalilinsu na fito da wannan, sun yi la’akari ne da karancin ilmin mata tun daga firamare zuwa sakandare har zuwa Jami’a, musamman a arewacin kasar nan, da Najeriya gaba daya, kididdiga da masana suka bayar kan ilimin mata ne ya sanya suka tashi tsaye su gina Jami’ar mata zalla ko hakan zai iya sanya a shawo kan yanayin da al’umma suka fada na koma-baya.
Ya cigaba da cewa, kwamitin ya kammala shirye-shirye guda uku game da Jami’ar, na farko dai Jami’a ce ta mata zalla da za su karancin ilmin kiyon lafiya, tana da sassa daban-daban. Inji M,aidoki.
Ya  cigaba da cewa, na biyu sun yi tsarin aiki na shirin Jami’a da kuma yadda aikin zai zama gamsasshe a karbe shi a matsayin Jami’a. Na ukun auna aikin da duba shi a matakin farko, wadanne abubuwa ne Jami’ar ke bukata, da sanin kasafin abin da za a kashe tun daga farkon aiki har kammala shi, da tabbatar da tsarin gudanarwa zai tafi ne yadda hukumar kula da jami’o’i ta kasa ta amince da shi ne. Wannan ne halin da ake ciki yanzu.” A cewar Malam Lawal.
‘An kammala matakin farko, an soma na biyun, shi ne fadada kwamiti a shigo da masu dukiya da fahimta don ganin wannan aikin ya samu nasara da ganin ba a kauce wa tsarin hukumar kula da jami’o’i ta kasa ba, da gayyato masana gogaggu cikin aikin don su taimaka. Sanin wurin da za a gina Jami’ar Sarkin Musulmi ne kawai zai fada maka wannan, lokacin kammala wannan aikin ya danganta da cika sharuddan hukumar  kula da jami’o’i (NUC) ta Nijeriya.’ inji Maidoki.
A jawabinta, Shugabar hukumar  UNICEF a Najeriya Jean Gough, ta ce hukumarta ta hada kai ne da Gidauniyar Sarkin Musulmi domin shirya wannan taro domin nuna wa iyaye mahimmancin ilmantar da ‘ya’ya mata.