Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal

A yanzu duk wani ɗan siyasar da ya san abin da ya kamata, ba zai koma jam’iyyar APC ba.

Dalilin da ’yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa APC — Tambuwal

Gwamnan Sakkwato; Aminu Waziri Tambuwal

Tsohon Gwamnan Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya bayyana cewa guguwar sauyin sheƙa da ta fara kaɗawa a tsakanin jam’iyyun siyasa a Arewa maso Yammacin ƙasar na da alaƙa da son zuciyar ’yan siyasar yankin.

Tambuwal ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a taron ƙusoshin jam’iyyar PDP da ya gudana yau Asabar a Jihar Kaduna.

Tambuwal ya zargi ’yan siyasar da ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki a ƙasar da son zuciya waɗanda ya ce ba sa kishin al’umma.

Tsohon gwamnan ya ce akwai dalilai da ’yan siyasa ke sauya sheƙa daga wannan jam’iyyar zuwa wata, “sai dai abin da na fahimta shi ne galibi ’yan siyasar na yin hakan ne ba don kishin al’umma ba face sai don buƙatunsu na ƙashin kai.

“Sannan kuma a yanzu duk wani ɗan siyasar da ya san abin da ya kamata, ba zai koma jam’iyyar APC ba saboda ƙuncin rayuwa da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta jefa ’yan Nijeriya a ciki.

Tambuwal wanda ƙusa ne a jam’iyyar PDP a Nijeriya, ya caccaki Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin APC da cewa ba ta wata madafar kamawa ballanta sanin inda ta dosa haɗi da rashin tausayin ’yan ƙasar.

Sanatan Sakkwato ta Kudu ya yi kira ga duk jam’iyyun adawa a ƙasar da su haɗa ƙarfi domin kawo wa ’yan Nijeriya sauyin da suke buƙata a Zaɓen 2027.

Aminiya ta ruwaito cewa, daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci taron akwai tsohon Gwamnan Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi da takwaransa na Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da tsohon ɗan takarar Gwamnan Jigawa, Mustapha Sule Lamido da Sanata Lado Dan Marke, da Honarabul Isa Ashiri Kudan da Ango Abdullahi da Shugaban Matasa na PDP, Muhammad Kadade Suleiman da sauransu.

 

Majalisar Wakilai ta ba da umarnin rufe shafukan intanet na batsa

Manyan makarantu sun shiga yajin aiki a Adamawa

Sanƙarau ta kashe mutum 26 a Kebbi

Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato