Dalilin da Yar’Adua ya soke cefanar da matatun mai da Obasanjo ya yi

Farashin da Obasanjo ya yi gwanjon matatun man Kaduna da Fatakwal bai kai kashi hudu na darajar kuɗinsu ba, kamar yadda Femi Falana ya bayyana

Dalilin da Yar’Adua ya soke cefanar da matatun mai da Obasanjo ya yi

Marigayi, Umaru Musa Yar’Adua, tsohon Shugaban Kasar Najeriya

Babban Lauyan Najeriya kuma ɗan gwagwarmayan kare haƙƙin da Adam, Femi Falana, ya bayyana cewa tsohon Shugaba Ƙasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya soke cefanar da matatun mai da Gwamnatin Obasanjo ta yi ne saboda ya saɓa doka kuma akwai maƙarƙashiya a ciki.

Femi Falana ya bayyana cewar, Obasanjo ya sayar da kashi 51 na hannun jarin Matatun man Kaduna da Fatakwal ne a kan Dala miliyan 160, alhali masu ruwa da tsaki sun yi amanna cewa darajar kuɗinsu ya kai Dala biliyan biyar a lokacin.

Farashin Obasanjo ta cefanar da matatun bai kai kashi hudu na darajar kuɗinsu ba. Aminiya ta gano cewa Dala miliyan 160 bai fi kashi 3.2 cikin 100 na Dala biliyan biyar ba.

Babban lauyan ya ci gaba da cewa gwamnatin Obasanjo ba ta bi ƙa’ida ba wajen cefanar da matatun ba a shekarar 2007, lamarin da ya jawo ruɗani da kakkausar adawa daga masu ruwa da tsaki a ɓangaren mai a Najeriya.

Obasanjo ya cefanar da matatun ne ga Kamfanin Bluestar Oil, wanda wata haɗaka ce ta Rukunin Kamfanin Ɗangote da kamfanin Zenon Oil mallakin Femi Otedola da kuma kamfanin Transcorp.

Falana ya ce sayar da matatun a daidai lokacin da Obasanjo yake shirin sauka daga kan mulki ya jawo zargi daga ƙwararru da ma’aikata da ’yan kasuwan man fetur, inda suka yi imani cewa cefanar da matatun zai cutar da Najeriya ne.

Ya ce waɗanda suka ɗaga kara kan cefanar da matatun a lokacin sun haɗa da Kungiyoyin Ma’aikatar Man Fetur da Iskar Gas (PENGASSAN da IPMAN). A sakamakon haka suka tsunduma yajin aiki da ya tsayar da Najeriya cik, saboda adawa da cefanar da matatun da farashin da hanyar da aka bi da kuma lokacin da aka yi.

Ya tuna cewa ƙungiyoyin sun janye yajin aikin nasu a lokacin ne bayan Gwamnatin Tarayya ta ba su tabbacin za ta binciki lamarin.

Gamsuwar Gwmanatin Marigayi Yar’Adua da waɗannan dalilai ne ta sa ya soke cefanar da matatun da Gwamnatin Obasanjo ta yi.

Falana ya buƙaci ƙungiyoyin mai da su ci gaba da gwagwarmaya domin kare ’yan Najeriya da ma ɓangaren mai, yana mai cewa masu jiran a sayar musu da matatun man gwamnati su sauya tunani, su je su gina nasu kamar yadda Ɗangote ya yi.