Dalilin da ya sa muka yi Idi ranar Asabar —Dahiru Bauchi

Da safiyar ranar Asabar ne shahararren malamin Mususluncin nan Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya jagoranci Sallar Idi a harabar gidansa da ke birnin Bauchi, bayan ya bai wa mabiyansa umarnin ajiye azumi ranar Juma’a. Shehin malamina ya bayyana dalilan sa na daukar wannan mataki na yin Idi sabanin ranar Lahadi da Mai Alframa Sarkin Musulmi […]

Dalilin da ya sa muka yi Idi ranar Asabar —Dahiru Bauchi

Shaikh Dahiru Usman Bauchi a Lokacin da yayi hawan Idin sallah karama a daura da gidan sa a jihar Bauchi

Da safiyar ranar Asabar ne shahararren malamin Mususluncin nan Shaikh Dahiru Usman Bauchi ya jagoranci Sallar Idi a harabar gidansa da ke birnin Bauchi, bayan ya bai wa mabiyansa umarnin ajiye azumi ranar Juma’a.

Shehin malamina ya bayyana dalilan sa na daukar wannan mataki na yin Idi sabanin ranar Lahadi da Mai Alframa Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar na yin azumin 30 ne a wani jawabi da ya yi na ganin wata aka kuma aike wa mabiyan sa.

Da misalin karfe 12.15 na daren Juma’a ne dai Shaikh Dahiru ya bayyana matsayinsa yana mai cewa “labari ya zo mana sahihi an ga watan Shawwal, [don haka] gobe [Asabar] za a tashi da Idi, babu azumi tun da watan Ramadana ya kare yau [Juma’a]”.

Ganin jama’a masu yawa

A cewar Shaikh Dahiru Bauchi, dukkan sharuddan da ake bukata don ajiye azumi sun tabbata.

“Da ma hukuncin da aka ba mu shi ne wata yana tabbata in aka samu mutane adilai guda biyu sun ce sun ga wata kuma an tabbatar da adalancinsu, ko ko jama’a masu yawa”, inji malamin.

“Jama’a masu yawa inda take farawa daga an samu mutum biyar baligai masu hankali, to shi ke nan an samu jama’a mustafidah – su kuma ba a binciken adalcinsu.

“A nan cikin garin Bauchi mutum takwas sun gani. A Liman Katagum mutum 10 sun gani – faya kam ma yaron gidanmu ne.

“Mun samu labari a Geidam, Yobe ke nan, mutane da yawa sun ga wata; mun samu labarin wasu sun kai labarin sun ga wata gidan Shehu Gibirima wajen halifansa…

“Jama’ar Zariya sun aiko mana sun ce sun ga wata, labari ya same mu an ga wata a Yawuri da Zariya.

“Tun da jama’a da yawa sun gani a garuruwa da dama, ba maganar mutum biyar ba, kuma Allah Ya wajabta mana azumi Ya ce ‘yan kwanaki ne… to yau wannan watan ya kare”, inji shehin malamin.

‘Ba mu samu labari da wuri ba’

Ya kuma kara da cewa ya samu labari an sanar da Sarkin Zazzau, wanda shi kuma ya sanar da Sarkin Musulmi, amma jagoran al’ummar Musulmin na Najeriya ya ce ya riga ya sanar cewa ba a ga wata ba.

“Da mun samu labari sahihi da wuri, da sai mu dage mu gaya wa Sarkin Musulmi ya yi magana a rediyo; to ba mu samu labari da wuri ba…”

Bisa wadannan dalilai ne mabiyan Shaikh Dahiru Bauchi suka ce za su yi Idi ranar Asabar.

“Dogaro da wadannan hujjoji, Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (Allah Ya yarda da shi),  ya umarci sauran almajirai da muridai da sauran jama’a cewa ranar Asabar ce 1 ga watan Shawwal”, inji wani makusanci ga malamin, wanda ya kara da cewa, “domin ai babu da’a ga wani mahaluki cikin saba wa Ubangiji”.

Sabanin ra’ayi

Tuni Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da sanarwar cewa ba a ga wata ba a Najeriya don haka azumi 30 za a yi.

Da ma dai a lokacin da yake bai wa al’ummar Musulmi umarnin duban wata ranar Juma’a ta hannun Sakatare Janar na Majalisar Koli ta Addinin Musulunci a Najeriya, Sarkin Musulmin ya ce zai yi wuya a iya ganin wata saboda zai fadi ‘yan minutuna kafin faduwar rana.

Karshen watan Ramadana na bana ya zo da sabanin ra’ayi wajen ganin wata, inda wasu Muslmin ma tun ranar Juma’a suka yi tasu Sallar Idin.