Dalilin da yunwa ta yi katutu a Arewa —Gwamnati
Rashin tsaro da rashin lafiyayyen cimaka na daga cikin manyan abubuwan da ke jawo yaɗuwar cutar tamowa a yankin Arewacin
Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta bayyana mummunar cimma da rashin kula da lafiya yadda ya kamata a matsayin manyan manyan dalilan yaɗuwar cutar tamowa a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Daraktan Sashen Kula da Abinci Mai Gina Jiki a Ma’aikatar, Ladidi Bako Aiyegbusi, ta ce bayyana cewa rashin nagartaccen ayyukan kula da rashin ruwa mai tsafta da rashin samun lafiyayyen abinci da rashin tsaftar muhalli da rashin wadataccen abinci suna taka muhimmiyar rawa wajen yawaitar cutar tamowa a yankin.
“sauran sun haɗa da matsalar ta’addanci da gudun hijira da ma matsalar tsaro da ke hana kaiwa ga mutane masu rauni,” in ji ta.
Ladidi ta sanar da hakan a Taron Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu Bayar da Rahoton Kiwon Lafiya (ANHeJ), Karo na 8, wanda gudana a Abuja a ƙarshen mako.
Da take jawabi ta bakin wakiliyarta kuma jami’ar kula da lafiyar ƙananan yara ta ma’aikatar, Adenike Bayode, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai masu fuskoki daban-daban domin magance matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a Nijeriya.
A nasa ɓangaren, Hadiminsa Shugaban Ƙasa kan Kiwon Lafiya, Dr. Salma Ibrahim, ya ce Gwamnatin Shugaba Tinubu ta duƙufa wajen ganin al’ummar Nijeriya sun samu nagartaccen kiwon lafiya ba tare da la’akari inda suke ko ƙarfin aljihunsu ko jinsi ba.