Dalilin da za ki gwada sababbin sinadaran girke-kirge na Dangote

Masoya abinci daga sassan Arewacin Najeriya suna magana a kan sababbin sinadaran girki masu inganci da Kamfanin Dangote yake sana’antawa. Kamfanin NASCON Allied Plc, wani vangare na fitaccen kamfanin na Dangote a kwanakin baya ya qaddamar da wasu sababbin sinadaran dafuwar abinci a kasuwa. Uku daga cikin sinadaran dafuwar abincin na Dangote sun hada da […]

Dalilin da za ki gwada sababbin sinadaran girke-kirge na Dangote

L-R: NASCON Allied Industries Plc, Group Managing Director, Paul Farrer; Dangote seasoning’s Brand Ambassador, Hadiza Gabon; NASCON Allied Industries Plc, Executive Director Commercial, Fatima Aliko Dangote; Director Hamis investment, Hamisu Rabiu; Dangote Industries Limited, Executive Director, Halima Aliko Dangote, at the unveiling of the new Dangote Seasoning Classic Cube, in Kano, Kano State, recently

Masoya abinci daga sassan Arewacin Najeriya suna magana a kan sababbin sinadaran girki masu inganci da Kamfanin Dangote yake sana’antawa. Kamfanin NASCON Allied Plc, wani vangare na fitaccen kamfanin na Dangote a kwanakin baya ya qaddamar da wasu sababbin sinadaran dafuwar abinci a kasuwa.

Uku daga cikin sinadaran dafuwar abincin na Dangote sun hada da dunkulen sinadarin girki na Dangote Seasoning Classic Cubes da garin sinadarin girki na Dangote Seasoning Stew Mid Powder da kuma kori na Dangote Curry Powder wadanda aka yi su musamman don dacewa da dandanon girki irin na mutanen Arewa.

Matan Arewa da masoya abinci mai dadi irin girkin Arewa a sassan kasar nan suna kiran wadannan sinadaran girki da Karshen Magana, kuma dalilin ba a boye yake ba.

Sababbin sinadaran girki na Dangote ba suna samar da dandano mai dadi ba ne kawai, har ma da kanshi da zakin da mutane suke so, kuma suna da saukin samu ga duk dan Najeriyar da yake son miya mafi dadi a duk lokacin da yake so.

Kamfanin ya gudanar da cikakken bincike wajen samar da sinadaran domin dacewa da nau’o’in miya da girkin da mutane Arewa suke bukata, kuma tuni kwalliya ta fara biyan kudin sabulu idan aka lura da yadda sinadaran suka samu gagarumar karbuwa cikin kankanen lokaci da gabatar da su.

A bayanin Babbar Darakta, Harkokin Kasuwanci na Kamfanin Kayayyakin Abinci na NASCON Allied Plc, Hajiya Fatima Aliko Dangote, ta ce jerin sababbin sinadaran girkin sababbin abubuwa ne da aka samar bayan daukar shekaru ana gudanar da bincike da bunkasawa. An samar da su ne daga ganyayyaki da tsirrai na musamman domin masoya abinci mai dadin dandano.

Don haka; hanzarta amfani da su a Miyar Taushe ko Kubewa ko kuma nau’o’in dafuwar shinkafa ko duk wani abinci mai sanya santi na abincin gargajiya na mutanen Arewa, sababbin sinadaran na Dangote za su sanya a cinye abincin har a sude kwano!

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara

Ɗan shekara 60 ya rasu bayan faɗawa a rijiya a Kano