Dalilin da za mu ba yankunan karkara muhimmanci wajen zuba jari — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano na tabbatar da cewa babu wata al’umma da za a bari a baya wajen ci gaban jihar.

Dalilin da za mu ba yankunan karkara muhimmanci wajen zuba jari — Gwamnatin Kano

Kwamishinan Raya Karkara da Ci gaban Al’umma na Jihar Kano, Abdulkadir Abdussalam, ya bayyana cewa fiye da rabin al’ummar jihar, kimanin kashi 55 cikin 100 na mutane miliyan 20.5, na rayuwa ne a yankunan karkara, lamarin da ya nuna buƙatar ƙara zuba jari a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, ilimi da noma.

Abdussalam ya bayyana hakan ne a taron Raya Karkara (RUSCODS 2026), inda ya ƙaddamar da Tsari da Dabarun Raya Karkara da Ci Gaban Al’umma Mai Ɗorewa na Jihar Kano (2026–2030).

Ya ce shirin wanda za a aiwatar cikin tsawo shekaru biyar zai rage talauci a karkara da kashi 40 cikin 100 nan da shekarar 2030 ta hanyar tabbatar da zuba jari a muhimman fannoni.

A cewarsa, fiye da kashi 55 na al’ummar Kano na rayuwa ne a ƙananan hukumomi 36 na karkara, inda noma ke zama babban tushen rayuwa kuma ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar.

Ya ƙara da cewa an ƙirƙiri wannan tsari ne bisa bayanan da aka tattara daga fiye da al’ummomi 300 da gidaje sama da 9,000 a ƙananan hukumomin karkara.

Abdussalam ya ce duk da irin zuba jarin da aka yi tsawon shekaru, har yanzu al’ummomin karkara na fuskantar matsalolin talauci ta fannoni da dama, ƙarancin ababen more rayuwa da kuma ƙarancin ayyukan gwamnati.

Ya bayyana cewa sabon tsarin ya mayar da hankali kan muhimman fannoni bakwai da suka haɗa da lafiya, ilimi, noma, ababen more rayuwa, kariyar zamantakewa, tsaro da kuma sauyin yanayi.

A cewarsa, aiwatar da shirin zai fara ne da ƙarfafa hukumomi a shekarar 2026, sannan a fara ayyukan gaggawa a 2027, a faɗaɗa ayyukan ababen more rayuwa zuwa 2029, kafin a tabbatar da aiwatar da cikakken shirin a tsakanin al’umma a shekarar 2030.

Ya ce za a samar da kuɗaɗen aiwatar da shirin ne daga kasafin kuɗin gwamnati da ƙananan hukumomi, tallafin Gwamnatin Tarayya, hukumomin ba da tallafi, abokan hulɗar ci gaba da gudummawar al’umma, ba tare da karɓo bashi ba.

Da yake jawabi, Sarkin Karaye, Muhammad Mahraz, ya buƙaci gwamnati ta fi mayar da hankali kan aiwatar da manufofin ci gaba, yana mai cewa yawancin tsare-tsaren da aka yi a baya sun tsaya ne a takarda.

Sarkin ya bayyana noma, ilimi, lafiya, ababen more rayuwa na karkara da ƙarfafa matasa a matsayin muhimman fannoni da ke buƙatar kulawa ta musamman.

Ya kuma nuna damuwa kan ƙaruwar talauci, rashin aikin yi, ƙaruwar yara da ke watsi da karatu da makaranta, ƙaura daga karkara zuwa birane da kuma ƙaruwar masu buƙata ta musamman da ke yin bara a kan tituna.

“Mun san matsalolinmu. Abin da muke buƙata yanzu shi ne aiwatar da tsare-tsare tare da samar da isassun kuɗaɗe. Duk wani tsari ba tare da an aiwatarwa ba zai ci gaba da zama a takarda ne kawai,” in ji Sarkin.

Ya kuma yi kira da a ƙara zuba jari a hanyoyin karkara, wutar lantarki, ruwan sha mai tsafta da tsaro domin bunƙasa tattalin arziki da rayuwar al’ummomin karkara.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda mataimakinsa, Murtala Sule Garo, ya wakilta, ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na tabbatar da cewa babu wata al’umma da za a bari a baya wajen ci gaban jihar.

Ya ce gwamnati za ta ci gaba da zuba jari a hanyoyin karkara, samar da ruwa, kiwon lafiya, ilimi, noma da ƙarfafa matasa, tare da ƙara haɗin gwiwa da abokan hulɗar ci gaba, kamfanoni masu zaman kansu, sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin farar hula.

Gwamnan ya buƙaci mahalarta taron su fito da shawarwari masu amfani da za su inganta ayyukan gwamnati, faɗaɗa damar tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar al’ummomin karkara a faɗin Jihar Kano.