Dalilin da za mu waiwayi batun raba Masarautar Kano — Kwankwaso

Za mu duba mu yi abin da ya dace a kan rarraba Masarautar Kano da Ganduje ya yi.

Dalilin da za mu waiwayi batun raba Masarautar Kano — Kwankwaso

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jazaman ne su sake bibiyar batun raba Masarautar Kano da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya yi.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da manema labarai ta kimanin sa’o’i biyu a Yammacin ranar Alhamis.

Kwankwaso ya tabo lamura da dama, waɗanda suka haɗa da batun alaƙarsa da Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Ganduje.

Sai dai maganar gyara dokar masarautun jihar ce ta fi ɗaukar hankalin mutane da ake ta cece-kuce a kanta.

Idan ba a manta ba, tsohon Gwamna Ganduje ne ya raba Masarautar Kano gida biyar tare da tube rawani Sarkin Kano na lokacin, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

Sai dai bayan nasarar da jam’iyyar NNPP  ta samu a zaben shekarar da ta gabata kuma tabbatar da nasarar da Kotun Ƙolin ta yi a makon jiya, Kwankwaso ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf za ta yi nazari kan rarraba masarautar da aka domin aiwatar da abin da ya dace.

An tambayi Kwankwaso ko mai zai iya cewa game da lamarin Masarautun Kano, sai ya ce “Gaskiya yana ɗaya daga cikin abubuwan da ba a taɓa zama da ni a kai ba, amma kuma nasan dole za a zo a yi magana.”

“A duba a ga abin da ya kamata a yi a kai, gyara za a yi ko rusau za a yi,” in ji Kwankwaso.

Kwankwaso ya ce “ai gyara za a yi a kai a don haka dole za a yi nazari kan dokar.

“Akwai abubuwa da yawa kuma wannan tarko ne. Duk wadannan abubuwa da aka yi su da gayya an kawo su ne da wasu munanan manufofin da kowa da kowa a nan da masu sauraronmu sun sani.

“Wani lokacin za a kawo abubuwa na alheri sai su zama marasa kyau, wani lokacin kuma ka kawo abubuwan da babu alheri amma sai su rikide su zama alheri.

“Don haka abin da na sani shi ne har yanzu ba a tuntube ni ba amma tabbas za mu zo mu tattauna mu ga abin da ya kamata a yi.”

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara