Dalilin daure ni a Kirikiri na zama dan wasan barkwanci – kulun Jalingo
Salisu Sulaiman, dan wasan barkwanci ne da ake wa lakabi da ‘kulun Jalingo.’ Ya shahara a wasan barkwanci da yake gabatarwa a gidan wasan kwaikwayo na kashin kansa a garin Agege, Legas. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana irin fadi tashin da ya sha da kuma irin kalubalan da yake fuskanta a sana’arsa: Ko za […]
Salisu Sulaiman, dan wasan barkwanci ne da ake wa lakabi da ‘kulun Jalingo.’ Ya shahara a wasan barkwanci da yake gabatarwa a gidan wasan kwaikwayo na kashin kansa a garin Agege, Legas. A tattaunawarsa da Aminiya, ya bayyana irin fadi tashin da ya sha da kuma irin kalubalan da yake fuskanta a sana’arsa:
Ko za ka fara da gabatarda kanka a takaice?
Kamar yadda na fada da farko, sunana Salisu Sulaiman kuma ana yi minii inkiya da kulun Jalingo. A Jihar Jigawa aka haife ni kuma na girma ne a garin Jalingo. Tun ina dan karami mutane ke kira na da kulun Jalingo saboda irin kamanceceniyar da nake da ita da marigayi Shu’aibu kulu.
Ta yaya ka samu kanka a sana’ar wasan kwaikwayo?
Da fari dai sana’ar sayar da atamfa nake yi a Kasuwar Kwari ta Jihar Kano, daga nan na gangaro Kurmi shekaru 12 da suka wuce. Na ci gaba da sayar da atamfa da takalman mata da leshi, kwatsam sai wata rana ’yan kai-kai (jami’ai masu hana saye-da-sayarwa a kan titunan Legas) suka kama ni, suka kai ni gidan kurkukun Kirkiri, sai na kira wata mawakiyar fina-finan Hausa, Murjanatu ’Yarbaba, na fada mata halin da nake ciki. Nan take ta kira wasu sojoji suka zo suka yi beli na a kan kudi Naira 11,500.
Da na fito na zauna ba sana’a, domin ba ni da jari, ba cin yau ba na gobe; sai na shiga wani gidan dirama a Unguwar Agumalu a Legas. Daga bisani na dinka rigar Fafalolo mai launin fari da kore, na fara zagayawa, duk inda na ga taron jama’a sai na je na yi musu wasan barkwanci da wasan kacakaura. Nakan je taron suna ko na siyasa ko makamancin haka, domin na sami taro da kwabo. Nakan samu Naira 3,000 ko ma fin haka a rana.
Da ma can kana da alaka da ita Murjanatu ’Yarbaba ne?
Biyayya ce da zama lafiya da jama’a kawai. Da ma ina da lambarta, nakan kira ta mu gaisa, kasancewar ni ma ina jin Filatanci. To da haka ne muka yi sabo da ita.
To yanzu ga ka da gidan wasa naka a nan Legas, ko ya haka ta kasance?
A lokacin da na zama dan gari a Apapa sai na ga bai dace ba yau na je can a ba ni, gobe ma na je a ba ni ko na yi wasa ko ban yi ba; sai na ga ai ko ubana ne, in ya ba ni yau ya ba ni gobe; ya ce in tashi in je in nemi na kaina. Kuma da ma can ni mutun ne mai son neman na kansa, haka ya sa na baro Unguwar Apapa na zo nan Abbatuwa na ci gaba da harkokina, har Allah Ya hada ni da wani maigidana, ya bude mana gidan dirama, muka ci gaba da harka.
Bayan na yi aiki da shi na tsawon shekara uku, na ga ban tsinana wa kaina komai ba, domin shi bai san ciwon ’yan wasa ba, bai san darajar bakin ’yan wasan da nake gayyatowa ba; ni nake yin komai. Wata rana na dau Naira 100 na sha shayi sai ya yi ta yi mini fada.
Da na ga ya kure mini hakurina sai na tara ’yan wasan da ke karkashina na fayyace masu komai. Na ce masu kar ku ga kamar da ni ake zaluntarku, don ni kaina hakuri nake yi. Na fada musu cewa ni na sa kaina a harkar, don haka na bar ta. Irin zaman lafiyar da nake yi da jama’a sai wasu ’yan kasuwa, akwai wanda ake kira Giwa da Babannan da Umaru suka saya mini fili, suka ce na ci gaba da harkata.
Haka kuwa aka yi, daman ni ne da jama’a manya da matasa da yara kowa nawa ne, za ka ji kowa yana ce mini kulu Ciyaman, kulun Jalingo. To ka ga haka muka ci gaba da harkar. Da man su ’yan kasuwa ne kuma ’yan Arewa. Sun san samu, sun kuma san rashinsa. In mun samu mu ci, in ba mu samu ba mu hakura har Allah Ya kawo.
Wane irin shirye-shirye kuke gabatarwa a gidan wasan naku?
Muna da shirye-shirye kusan kala 20, duk hanyar da zan bi na bai wa ’yan kalo dariya domin na yaye masu bakin ciki na san ta. Ban da wasan barkwanci da na kacakaura, ina yin wakoki kala-kala kuma muna yin rawa a nan mazanmu da matanmu. Ina da yaran wasa su kusan 30 kuma nakan gayyato manyan ’yan wasa daga Arewa da kasar Ghana. Kadan daga cikin ’yan wasan Hausa da na gayyato sun hada da Shu’aibu Kumurci, Baba Ari, dan Auta da ’Yar auta, Musa Mai Sana’a da dai makamantansu.
Ba kuma komai ya sa haka ba illa biyayyata a gare su, domin duk sanda nake da sha’awar gayyato daya daga cikinsu, zan kira lamba, na ce kulu Ciyaman ne mai gidan wasa a Abbatuwa. Saboda irin daraja su da mutunta su da nake yi, sai ka ga sun zo sun yi mini wasan kwana uku ko ma fin haka.
Ko akwai wani kalubale da kake fuskanta a wannan sana’ar?
Akwai wani lokaci da marigayi Rabilu Musa dan Ibro ya zo za mu yi wasa a Apapa, da na shiga dakin shirya ’yan wasa; na yi shiri. Da ya gan ni sai jikinsa ya yi sanyi, ya kasa matsowa inda nake saboda yana tunawa da marigayi kulu, dalilin kamanceceniyata da kulu, domin in ka gan ni kamar an tsaga kara ne. Da na fuskanci haka sai na janye jikina na fita daga gidan wasan, domin ba na nufin na bata masa hanyar neman abincinsa.
Ganin yadda mutane suke ce mini kulun Jalingo ne na yanke shawarar shiga wasan barkwanci domin ribar sana’a romonta. Matsala ta biyu da nake fuskanta ita ce karancin ’yan kasuwar da za su tallata ni, duniya ta san ni, domin na shirya wani fim mai suna ‘Kowa Da Kiwon Da Ya Karbe Shi’ amma a sakamakon rashin furodusa da ’yan kasuwar da za su tallata fim din bai wuce Jihar Legas ba sai ’yan daidaikun da suka saya suka kai Arewa.
Ni a yanzu burina duniya ta san ni, ba wai na samu kudi ba. Muddin zan samu wanda zai zo ya kafa mini kyamara, ya dauke ni ko’ina ne zan yi masa wasa; matukar zai cika mini cikina da abinci, ’yar matsalata ta Naira 10 ko 200, ya magance ta, bukatata ke nan, ba ni da dogon buri.
Wane alfanu ka samu a wannan sana’a ya zuwa yanzu?
Alhamdu lillahi, da sana’ar wasan barkwanci na gina gida, na yi aure kuma a cikinta nake taimaka wa iyayena da ’yan uwa da abokan arziki.