Dalilin dawo da Farfesa Bogoro kan Shugabancin Asusun TETFund

An sake nada Farfesa Suleiman Elias Bogoro a matsayin Babban Sakataren Gidauniyar Tallafa wa Manyan Makarantu ta Kasa (TETFund), bayan Gwamnatin Tarayya ta sauke wanda ke kan kujerar, Dokta Abdulllahi Garba Bichi. Lamarin wanda ya zo a ba-zata yana zuwa ne shekara biyu bayan gwamnatin Buhari ta dakatar da shi daga mukamin a watan Fabarairun […]

Dalilin dawo da Farfesa Bogoro kan Shugabancin Asusun TETFund

An sake nada Farfesa Suleiman Elias Bogoro a matsayin Babban Sakataren Gidauniyar Tallafa wa Manyan Makarantu ta Kasa (TETFund), bayan Gwamnatin Tarayya ta sauke wanda ke kan kujerar, Dokta Abdulllahi Garba Bichi.

Lamarin wanda ya zo a ba-zata yana zuwa ne shekara biyu bayan gwamnatin Buhari ta dakatar da shi daga mukamin a watan Fabarairun shekarar 2016, tare da maye gurbinsa da wanda ta dakatar a yanzu.

Labarin nadin nasa ya bayyana ne a ranar Litinin da ta gabata bayan ya isa ofishin da takardar tabbaccin nadin, sannan daga bisani Ma’aikatar Ilimi wadda gidauniyar ke karkashinta ta fitar da bayanin da ya ruwaito Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu da bayanin cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da nadin Bogoro da kuma fara aiki nan take.

Takardar wacce ke dauke da sa hannun Babban Sakataren Ma’aikatar da kwanan wata 21 ga Janairun ban da aka mika ga Farfesa Bogoro tana da taken “Sake nada Farfesa Bogoro a matsayin Babban Sakataren Gidauniyar TETFund,” ta kuma yi bayanin cewa: “Sake nadin naka zai kasance ne na wani sabon wa’adi na tsawon shekara 4 gwargwadon gamsuwa da aikin da za ka aiwatar.”

Farfesa Bogoro dai ya fara zama Babban Sakataren Gidauniyar ce a watan Afirilun shekarar 2014, lokacin da tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya nada shi. Rahotanni sun ce nadinsa na wancan lokacin ya biyo bayan gabatar da sunansa ne da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP  ta Kasa, Alhaji Ahmadu Adamu Mu’azu ya yi ga Jonathan.

Farfesa Bogoro ya fito ne daga Karamar Hukumar Bogoro, shi kuma Alhaji Adamu Mu’azu ya fito ne daga Karamar Hukumar Tafawa Balewa, kananan hukumomi 2 da suka kasance a yanki guda na Kudancin Jihar Bauchi. Tini dai Mu’azu ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC.

Bayan dakatar da shi a baya, Bogoro ya koma Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, ya ci gaba da aikin koyarwa kamar yadda yake a baya.

 

Mabambantan ra’ayoyin da suka biyo bayan sake nadin nasa

Aminiya ta gano cewa murnar dawowarsa kan mukamin na dauke da mabambantan ra’ayoyi a jiharsa ta Bauchi, musamman ma daga bangaren ’yan siyasa. A yayin da wadansu ke danganta lamarin da gagarumin aikin da ya aiwatar a lokacin da ya shugabanci asusun a baya, wadansu na ganin sake nadin nasa wata dabarar siyasa ce ta karfafa tasirin Jam’iyyar APC mai mulki a Jihar Bauchi da ake ganin ficewar Shugaban Majalisar Wakilai, Yakubu Dogara daga jam’iyyar zuwa PDP ya yi mata illa, musamman a yankin Kudancin jihar, inda yake da karfin tasiri a siyasance.

Sai dai dawowar Mu’azu Jam’iyyar APC da sake nada Bogoro kan mukaminsa, wanda na gaba-gaba ne a cikin jagororin yankin, masu hasashe na ganin cewa hakan zai kara karfafa damar nasarar jam’iyyar, musamman a yankin da kuma jihar baki daya. Wani jigon siyasa daga Jihar Bauchi ya bayyana cewa “Ba ni da tababa a kan zai tabbatar da cewa ya yi dukan mai yiwuwa da bai saba ka’ida ba wajen ganin nasarar jam’iyyar a jihar, a matsayinsa na wanda ta nada shi. Lallai Dogara na da matukar tasiri, sai dai shi ma Farfesa yana da nasa kuma daidai yake da shi.”

Wani malami a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, Simon Yalams da suka yi aiki tare da Farfesa Bogoro a makarantar da kuma wani tsohon Kwamishina a Jihar, Dokta Audu Ghani Bogoro sun bayyana cewa duk da dai wadansu za su rika ganin lamarin ta fuskar siyasa tare da neman danganta shi da hakan, kasancewar ana lokacin kakar siyasar, suna da yakini a kan batun cancanta na gaba a lamarin, kuma shi ne babban abin da gwamnatin ta fi yin la’akari da shi wajen sake nada shi.

 

Dalilan dakatar da Dokta Bichi da martanin da ya mayar

Kodayake ba wani bayanin da gwamnati ta fitar a matsayin dalilin sauke shi daga kan mukamin ba, wasu majiyoyi sun bayyana wa Aminiya cewa dalilai da dama sun taka rawa a lamarin. Bayanai sun ce Dokta Bichi wanda ke matsayin Babban Darakta a wata kungiyar goyon bayan Shugaban Kasa Buhari a zabe da ke tafe mai suna “One2Tell10 Buhari Support Group” ya samu rashin jituwa da Ministan Ilimi a kan yadda za a tafiyar da kudin asusun, sannan kuma yana botsare wa wasu umarni da suka fito daga ma’aikatar.

Wadansu sun ce ya kutsa harkar siyasa fiye da kima, musamman ma a jiharsa ta Kano, ta yadda hakan ke hana shi gudanar da ayyukansa kamar yadda ya dace.

Dokta Bichi dai ya taba rike mukamin mai taimakawa na musamman ga Ministan Ilimi gabanin a nada shi Babban Sakataren asusun a shekarar 2016. Sai dai a martanin farko da ya bayar t sashin Hausa na BBC a ranar Larabar da ta gabata, a shirinsu na safe, korarren Sakataren ya musanta  dalilan da aka dangatar lamarin da su.

Ya ce ya fi zama a Ma’aikatar Ilimi fiye da ofishinsa ne “Kasancewar kusan ayyuka 2 ne nake yi, ina aikin asusun  kuma ina yin ayyukan Minista. Ashe ke nan a ce bai iya samuna ba gaskiya ba ce,” inji shi.

Dokta Baffa ya ce abu guda da ya sani shi ne, Ministan ya jima yana ci masa dundunniya a wajen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari amma Shugaban ya jure ba tare da ya biya masa bukatarsa ba sai a wannan karo, inda ya ce ya je masa da bukatar a maye gurbinsa a ranar Juma’a da ta gabata a lokacin da ya samu damar ganawa da shi.

 

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta