Dalilin dawo da hoton Sanusi a dakin taron gidan gwamnatin Kano

Gwamnatin ta bayyana ainihin dalilin da ya sa ta dawo da hoton

Dalilin dawo da hoton Sanusi a dakin taron gidan gwamnatin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sake dawo da hoton tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a dakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnatin Jihar.

An dai gina dakin ne a shekara ta 2014, zamanin tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, lokacin da aka nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano na 14.

A lokacin dai, an yi amfani da sabon dakin wajen nada sabon Sarkin da kuma bikin ba shi sandar mulki.

Sai dai a wani bangare ne kwaskwarimar da sabuwar gwamnatin Jihar take yi wa dakin taron, hotuna sun bayyana da ke nuna hoton tsohon Sarkin a cikinsa. Lamarin dai ya yi ta jawo ce-ce-ku-ce, musamman ga wadanda ke ta rade-radin cewa za a dawo da tsohon Sarkin kan kujerarsa.

To sai dai a cewar Sakataren Yada Labaran Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, an saka hoton na shi nee da nufin ci gaba da tuna wa da shi kasancewar saboda nada shi aka gina dakina 2014.

Ya ce hakan zai sa tarihin ya ci gaba da kasancewa ko da kuwa wane ne yake sarauta, kodayake ya ce ba a saka hoton saboda wata manufa ba.

A cewar Kakakin na Gwamnan, shi kansa sake dawo da hoton na Sanusi, wani bangare ne na aikin sake fasalin shi domin mutanen da za su zo nan gaba su ma su san tarihin.

Ana ganin Sanusi dai a matsayin wanda yake dasawa da gwamnatin Jihar mai ci ta ja’iyyar NNPP, wacce Abba Kabir Yusuf yake yi wa jagoranci.

A watan Maris din shekara ta 2020 ce dai tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sauke Sanusi daga sarautar Kano, sannan ya maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi