Dalilin da ya sa ba a samu coronavirus a Kogi da Cross River ba
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce jihohin Kogi da Kuros Riba ne suke da mafi karancin mutanen da aka yi masu gwajin cutar coronavirus tun lokacin da ta bulla a Najeriya a watan Fabrairu. Zuwa yanzu dai jihohin ne kadai ne ba a samu ko da mutum daya da aka […]
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta ce jihohin Kogi da Kuros Riba ne suke da mafi karancin mutanen da aka yi masu gwajin cutar coronavirus tun lokacin da ta bulla a Najeriya a watan Fabrairu.
Zuwa yanzu dai jihohin ne kadai ne ba a samu ko da mutum daya da aka tabbatar yana dauke da cutar ba a fadin Najeriya.
Wannan yana kunshe ne a cikin wani rahoto da hukumar ta fitar ranar Talata.
A cewar rahoton, mutum daya ne aka yi wa gwajin cutar a jihar Kogi, yayin da ita kuma jihar Kuros Riba mutane bakwai kawai ta tura da sanfurinsu don yin gwajin.
Tun a watan Fabrairun bana ne dai aka samu mutum na farko da aka tabbatar yana dauke da wannan cutar a Najeriya.
A makon farko na wannan watan ne dai jami’an hukumar ta NCDC suka ziyarci jihar Kogi don tabbatar da ikirarin da take yi cewa babu wanda ya kamu da cutar a yankinta.
Lamarin ya janyo takaddama tsakanin bangarorin biyu, inda gwamnatin jihar ta yi umarnin dole sai jami’an hukumar ta NCDC sun killace kansu na tsawon makonni biyu kafin su fara aiki.
Kwamishinan yada labarai na jihar ta Kogi, Mista Kingsley Fanwo, ya yi zargin cewa jami’an hukumar sun ki yarda su killace kansu, daga baya kuma suka cika wandonsu da iska suka bar jihar.
Kwamishinan ya kuma yi ikirarin cewa jihar ta gudanar da gwajin a kan mutane 111 a kashin kanta ba tare da sa hannun hukumar NCDC ba.
Zuwa yanzu dai sama da mutane 6,000 ne a jihohi 34 da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya.