Dalilin gaza magance matsalar tsaro a Najeriya

Babban dalilin rashin nasara yaki da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga shi ne rabuwar kai tsakanin hukumomin tsaro, inji Ambrose Aisabor, tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.

Dalilin gaza magance matsalar tsaro a Najeriya

Masana harkar tsaro sun bayyana rashin hadin kai da aiki tare tsakanin hukumomin tsaro shi ne abun da ya sa yaki da ‘yan tayar da kayar baya da sauran matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriya.

Tsohon Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ambrose Aisabor wanda ya bayyana haka, ya ce maimakon jami’an tsaron su hada kai su yi aiki tare, sai suka bige da aiki a daidaikunsu.

Ya ce rashin hadin kan ya kara fitowa karara ne bayan mutuwar matukiyar helkwaftan yakin sojan saman Najeriya, Tolulope Arotile.

Ya ce sojojin sun kankane aikin ‘yan sanda wajen binciken musabbabin rayuwarta