Dalilin hana shiga da fita a Kano —Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya bayar da umarnin kafa dokar hana fita kwata-kwata ta mako biyu a Kano da nufin shawo kan annobar coronavirus wadda ke nema ta gagari hukumomi. Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi ga ’yan Najeriya da maraicen Litinin. “Dangane da Kano, na ba da […]

Dalilin hana shiga da fita a Kano —Buhari

Shugaba muhammadu Buhari na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya bayar da umarnin kafa dokar hana fita kwata-kwata ta mako biyu a Kano da nufin shawo kan annobar coronavirus wadda ke nema ta gagari hukumomi.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi ga ’yan Najeriya da maraicen Litinin.

“Dangane da Kano, na ba da umarnin tabbatar da dokar hana fita kwata-kwata har tsawon makwanni biyu kama daga yanzun nan.

“Gwamnatin tarayya za ta yi amfani da duk abin da ya kama na ma’aikata da kayan aiki don tallafa wa jihar ta shawo kan kuma ta taka wa annobar birki ta kuma hana yaduwarta zuwa jihohin makwabta”.

Kiraye-kiraye

Mai yiwuwa wannan mataki dai ya biyo bayan kiraye-kirayen da wasu sassan al’umma suka yi ne ga gwamnatin tarayya ta sa hannu a lamarin jihar ta Kano, wadda a baya-bayan nan ta fudkanci karuwar mace-mace.

Ko gwamnan jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ma, a wani mataki mai nuna alamun karfin hukumomin jihar ya kare, ya zargi gwamnatin ta tarayya ta juya wa Kanawa baya.

Yayin wata hira da ya yi da BBC, gwamnan ya koka da yadda aka dakatar da gwajin cutar da yadda yunkurinsa na ganin Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) da Ma’aikatar Lafiya ta tarayya sun yi wani abu ya ci tura.

Budaddiyar wasika biyu

A wata budaddiyar wasika da ya rubuta wa Shugaba Buhari, tsohon gwamnan jihar Dokta Rabiu Musa Kwankwaso ya yi kira ga shugaban kasar da ya dauki matakin gaggawa.

Ita ma wata gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar, a wata wasika da ta aike wa Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma jagoran Kwamitin Shugaban Kasa a Kan COVID-19, ta yi zargin cewa babu jagoranci a yakin da ake yi da annobar, tana kira ga gwamnatin tarayya ta shiga cikin lamarin.

Karuwar mace-macen da aka samu dai ta kara tayar da hankulan mutane a jihar, inda a karshen mako aka rasa wasu fitattun mutane, ciki har da manyan jami’ai da tsofaffin kusoshin gwamnati da shehunan malaman jami’a.

Sai dai kuma gwamnatin jihar, wadda ta ce tana sane da yawan mace-macen, ta jaddada cewa ba su da alaka da coronavirus.

Ana bincike kan lamarin

Kwamishinan Yada Labarai Kwamared Muhammad Garba ya ce gwamnati ta fara gudanar da bincike a kan lamarin don gano musabbabin yawan mace-macen.

“Duk da cewa ba a kai ga kammala bincike a kan lamarin ba, amma binciken farko-farko na Ma’aikatar Lafiya ya nuna cewa ba cutar coronavirus ce ke kashe mutanen ba, suna mutuwa ne saboda cututtukan hawan jini da maleriya da ciwon suga da kuma sankarau”, inji shi.

A cewar kwamishinan, Gwamna Ganduje ya kagu matuka da son ganin sakamakon rahoton binciken don sanin matakin dauka.

Tattaro bayanai

A yanzu haka dai gwamnatin ta ce ta fara tattaro bayanan mutanen da suka mutu daga iyalansu don gano musabbabin mutuwarsu.

Mataimakin Shugaban Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Yaki da Annobar Coronavirus a jihar, Dokta Sabitu Shuaibu, shi ne ya bayyana haka yayin wata ganawa da manema labarai.

Dokta Shuaibu ya ce tattaro bayanan wadanda suka mutun ne mafita don gano musabbabin mutuwar tasu.

A cewarsa dole ne a fuskanci irin wadannan mace-macen a yayin da aka mayar da hankali kan cutar coronavirus aka kuma yi shakulatin bangaro da sauran cututtuka.

Shugaba Buhari dai bai yi bayani a kan takamaimai me gwamnatin tarayya za ta yi don ceto jihar Kano ba.

Amma da yake an ce gani ya kori ji, a yanzu Kanawa sun zuba ido su ga matakan da ya yi alkawarin dauka don tsamo wa jihar kitse a wuta.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi