Dalilin jinkirin nada ministoci – Buhari

A lokacin ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Washington na kasar Amurka ya tattauna da Muryar Amurka inda ya yi tsokaci kan dalilin ziyarsa da lokacin da zai nada ministocinsa da kuma rikicin majalisa da Jam’iyyar APC: Kafin zuwanka nan Amurka jami’ai masu kula da yada labaranka sun ce akwai manyan bukatu uku, ko […]

Dalilin jinkirin nada ministoci – Buhari

A lokacin ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a birnin Washington na kasar Amurka ya tattauna da Muryar Amurka inda ya yi tsokaci kan dalilin ziyarsa da lokacin da zai nada ministocinsa da kuma rikicin majalisa da Jam’iyyar APC:

Kafin zuwanka nan Amurka jami’ai masu kula da yada labaranka sun ce akwai manyan bukatu uku, ko an samu biyansu a ganawar da ka yi da Shugaba Barack Obama?
Da farko ina so mutane su fahimci cewa akwai manyan kasashe bakwai da ake kira G7, sun kira ni taro a kasar Jamus, sun nuna min damuwarsu a kan tsaro a Najeriya musamman a yankin Arewa maso Gabas. Suka ce in gaya musu abin da ake ciki, suka yi alkawarin za su taimaka. Shi ya sa da na dawo, muka yi kokari muka rubuta abubuwan da muke bukata da barnar da ’yan Boko Haram suka yi na kona makarantu da asibitoci da karya gadoji da sauran barnar da suka yi. Sannan kuma kan kasashen gabar Tafkin Chadi wato Kamaru da Chadi da Nijar da Najeriya da Benin da ta yarda ta shigo cikinmu. Mun yi hedkwata a Ndjamena, babban birnin Chadi. Najeriya za ta ba da sojoji sauran kasashen ma za su ba da, ana tunanin inda za a sa su kuma za a kai su zuwa karshen wannan wata. To abin da muke fama da shi, shi ne a ba su kayan da motoci zuwa bindigogi. Sannan jiragen sama na yaki da sauransu. Wadannan bukatu ne na tattara za mu aikawa su manyan kasashen bakwai. Kuma na taho wa Shugaba Obama da kwafinsa. To yanzu a ce me aka yi, jiya na gan shi, sai an ba da lokaci tukunna.
Wane irin taimako Amurka za ta ba Najeriya ganin ita kanta ba ta magance irin wadannan matsaloli a kasashen da ta shiga kamar ba Afghanistan?
To ai abin da ya faru a Afghanistan da Siriya ba iri daya ba ne da na Najeriya. Najeriya ka ga mu akwai makwabtanmu Nijar da Chadi da Kamaru. Kuma duk wanda yake bin abin da ke faruwa ya ga yadda ’yan Boko Haram suke fada wa wadannan kasashe. Su tada bam, su je su zagaye sojojinsu su kashe su. An ce idan ana ta kai, ba a ta kaya. Saboda haka duka mun hada kanmu za mu yaki Boko Haram. Shi ne aka ce an hada wadannan sojoji da ake kira Multinational Joint Task Force.
Yawancin Boko Haram harin sari-ka-noke suke yi, abin da suke a Iraki ke nan, abin da suke a Afghanistan ke nan, ba ka saninsu, zuwa suke su dana bama-bamai su gudu, ko su zo cikin jama’a su tada nakiyoyi. Ta yaya Amurka za ta taimaka muku yayin da ita ba ta samu nasara ba a inda take yake-yake yanzu?
Taimakon da Amurka za ta yi shi ne ta koyar da sojojinmu da na ruwa da na sama da na kasa da ’yan sandanmu a kan abin da suka koya suka gani a wadancan kasashen da ka fadi, amma ka san akwai asali a Najeriya, akwai masu unguwanni, akwai dagatai, akwai hakimai, akwai sarakuna. Saboda abin da muke ta fada musu shi ne bakin fuskoki da wadanda suke shigowa daga ina suke. Wannan shi ne hanyar da za a samu a san wadanda suke wannan yakin na sari-ka-noke.
Wadanne irin dabaru kuka fito da su tun kama aiki da tsohuwar gwamnatin da ka gada ba ta yi aiki da su ba?
Tsohuwar gwamnati ba ta dauki abin da muhimmanci ba. Yaya za a yi a ce sojojin Najeriya wadanda suka yi yaki a kasar Bama da Kongo da Laberiya da Saliyo da Sudan a ce sun kasa sarrafa kananan hukumomi 14 cikin kananan hukumomi 774, kafin ma su fara yakin sari-ka-noken. Saboda haka gwamnatin da ta gabata ba ta da niyyar ta yi, ko ta ci yakin Boko Haram, amma mu muna da niyyar Boko Haram mun san yadda za mu yi da su da yardar Allah.
Tsohuwar Gwamnati ta fitar da kudi sosai domin yaki da Boko Haram kusan biliyoyi sun kai 30 na Dalar Amurka cikin shekara biyar, me ya sa za ku sayo kayan aiki duk da an fitar da wadancan kudi? Ko kuke neman taimako?
Na tabbata kun sha ji sojojin Najeriya su suke fadi da bakinsu cewa an tura su wajen fada, amma babu kayan aiki. Saboda haka kudin da aka tura an sayi kayan aiki ko ba a saye su ba.
An ce ka bukaci takardu daga wajen manyan hafsoshi game da yadda aka sayi makaman, haka ne? Kuma kananan sojoji suna kukan ka gudanar da bincike saboda manyansu sun azurta daga wannan harka ta Boko Haram?
Eh, za a bincika, za a bincika.
Ka yi maganar zuwanka ka gaji matsaloli. Ga matsala daya a majalisa, kuke da gwamnati, kuke da rinjaye amma an kasa fid da shugabanni. Akwai maganar cewa ka sa baki ciki don a warware wannan matsalar. Me ya sa ba ka sa baki ba a ciki?
Saboda majalisa ta dattawa da ta wakilai suna da hanyoyin zaben shugabanninsu. Amma kuma jam’iyya, jam’iyya ce. Tunda ta matakin jam’iyya suka ci zaben, to, dole su saurari jam’iyya. Saboda haka bai kamata in fito in sa baki ba. Amma a kan dan jam’iyya ne ni, ina magana da sauran shugabannin jam’iyya yadda ya kamata a tafiyar da wannan rikici tsakanin ’yan jam’iyya a majalisa ta dattawa da ta wakilai.
Ko kana ganin wadanda ka gaji mulki wajensu ba su yi daidai ba da suke zaben wadanda suke so su yi aiki. A ce ga wanda nake so ya zama shugaban Majalisar Dattawa, ga wanda nake so ya zama shugaban Majalisar Wakilai. Ana ganin da ka sa baki da duk wannan an kau da shi?
Haka ake gani, amma me ne ka’ida. ka’ida ’yan majalisa su aka ce su zabi shugabanninsu. Amma jam’iyya tana da magana a kanta. Saboda haka ko wane ne Shugaban kasa idan har yana so ya fadi  sunan wanda yake so ko wani abu, to, a yi aiki da jam’iyya. Ba Shugaban kasa ne zai fito ya ce shi ya fi karfin jam’iyya, ya fi karfin majalisa shi zai yi nadi ba. Sha’anin yin nadi bai kawo zaman lafiya. Dole a bi ka’ida.
Akwai cece-cuce dangane da kudin da ake rabawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da jihohi da kananan hukumomi. Akwai dan majalisar da ya tafi kotu yana cewa ba a bi ka’ida ba saboda majalisa ba su kasafta wadannan kudaden ba. Ina aka samu wadannan kudade kuma za ka tafi wajen majalisa domin kasafta su ko yadda aka raba su yanzu ya yi?
To ai akwai ka’idoji, ni dai abin da zan tabbatar shi ne zan goyi bayan a bi ka’ida. Saboda ko bayan na tafi kada a bar kura a baya.
Daga karshe me za ka ce game da aikace-aikacen kafofin watsa labarai?
Ina fata za ku rika yin bincike kafin ku fadi wasu labarai. Balle wadanda za su bata sunayen al’umma ko majalisa, ko ministoci, ko dai wani sashe na gwamnati. A tabbatar da labari tukuna.  
Ka rubuta wata makala a jaridar Washington Post cewa ba za ka nada ministoci ba sai cikin watan Satumba. Me ya sa ka dauki wannan matakin ganin wadanda suke sukar gwamnatinka suna da hujja cewa ka gama sanin komai, ba ka kuma son nada ministocin nan. Ka fi son aiki da wadannan da ke kasa da su?
Ka ga ni daya daga cikin matsalolinku ke nan ’yan jarida. Ko Amurka kuke zaune, ko a Najeriya. Akwai abin da ake kira ’yan jarida su rika yin bincike. Shekara 16 na PDP, majalisa takwas. Gaya mini wace gwamnati ta yi ministoci cikin wata biyu da aka zabe ta. Su ma ke nan balle mu da muka samu wannan katobara a kasa. Bayan mako biyu sai a rika cewa ba a yi minista ba.