Dalilin kara tsaurara matakan tsaro a Jos – STF

Sakamakon korafe-korafe da jama’ar Jihar Filato ke yi da tsaurara matakan tsaro da Rundunar Tsaro ta Musamman (STF) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar ta yi, rundunar ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu cewa mayakan Boko Haram sun shirya kai hare-hare a jihar.Kakakin Rundunar da […]

Dalilin kara tsaurara matakan tsaro a Jos – STF
Dalilin kara tsaurara matakan tsaro a Jos – STF

Sakamakon korafe-korafe da jama’ar Jihar Filato ke yi da tsaurara matakan tsaro da Rundunar Tsaro ta Musamman (STF) da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar ta yi, rundunar ta ce ta dauki wannan matakin ne sakamakon bayanan sirrin da ta samu cewa mayakan Boko Haram sun shirya kai hare-hare a jihar.
Kakakin Rundunar da ake kiranta da Operation Safe Haben (OPSH), Kyaftin Ikedichie Iweha ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin. “Mun tsaurara tsaron ne sakamakon samun bayanan sirrin cewa mayakan Boko Haram za su kai hare-hare a Jihar Filato, kuma a matsayin rundunarmu ta wadda aka dora mata alhakin samar da tsaro a jihar nan, ba za mu bari wani dan ta’adda ya rika tayar da hankalin mutane ba,” inji sanarwar.
Kyaftin Iweha ya ja hankalin mutane su rika lura da bakin abubuwan da ba su fahimce su ba, sannan su rika kai rahotan wadanda ba su yarda da take-takensu ba.
“Muna ba mutane shawara su rika sa ido a wuraren da ke jama’a ke taruwa, musamman masallatai da coci-coci da tasoshin mota da wuraren shakatawa da na wasanni. Masu lura da wuraren shakatawa da wasanni da kuma shugabannin kasuwanni da masallatai da coci-coci su tabbatar sun sanya lura da wurarensu,” inji sanarwar.
Kyaftin Iweha ya tabbatar da cewa sun samu irin wadannan bayanan sirri kuma sun tashi tsaye wajen ganin sun bata duk wani shiri na wadanda suke neman tayar da zaune tsaye.
A karshe ya bukaci jama’ar jihar su rika ba jami’an tsaro hadin kai wajen gudanar da bincike don ganin cewa zaman lafiya ya tsaya da kafafunsa a jihar.