Dalilin nada ni sarautar Magawatan Dutse – Magawata Salihi Suleiman
Sarautar Magawata sabuwar sarauta ce mai daraja a Masarautar Dutse kuma ana bayar da ita ce ga wanda yake hidima wa al’umma da addini. Maga hakimi ne da aikinsa ya rika tattara bayanan ganin wata a lokacin watan azumi daga yankunan masarautun hakimai da dagatai na masarautar, shi kuma ya sanar da ’yan Kwamatin Shura […]
Sarautar Magawata sabuwar sarauta ce mai daraja a Masarautar Dutse kuma ana bayar da ita ce ga wanda yake hidima wa al’umma da addini. Maga hakimi ne da aikinsa ya rika tattara bayanan ganin wata a lokacin watan azumi daga yankunan masarautun hakimai da dagatai na masarautar, shi kuma ya sanar da ’yan Kwamatin Shura su kuma su sanar da Mai martaba Sarki cewar an ga watan azumi ko na Sallah.Wakilin Aminiya ya tattauna da Alhaji Salihi Suleiman Birnin Kudu, Magawatan Dutse kan wannan sarauta ta Magawata da Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Muhammad Nuhu Sanusi ya nada shi:
Takaitaccen tarihin rayuwa
Sunana Salihi Suleiman Birnin Kudu, an haife ni a garin Birnin Kudu a 1956 na yi karatun firamare a Santaral ta Birnin Kudu daga nan na wuce Makarantar Sakandaren Rano bayan na gama sai na wuce Kwalejin Rumfa, bayan na gama Rumfa a 1974 shi ne na wuce Samaru inda a nan ne na yi satifiket a kan aikin gona. Daga nan ne na fara aiki a matsayin malamin gona ina kula da yankin Dutse da Gundumar Kiyawa a lokacin ba sa matakin kananan hukumomi. Daga baya na koma Karamar Hukumar Birnin Kudu
Na rike mukamai daban-daban ciki har da babban jami’i a Makarantar Horar da Malaman Gona na rike matakin horar da malaman gona mai bai wa kananan malaman gona horo a bangaren karatu kuma na yi babbar diploma (HND) a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.
Bayan da na kammala aikin gwamnati, Sakamakon yadda na yi kokarin zama da jama’a lafiya da irin gudunmawar da na bayar a fada ya sa Mai martaba Sarkin Dutse ya nada ni hakimi a matsayin magawatan Dutse.
Mene ne asalin wannan sarauta taka?
Sarauta ce sabuwa Mai martaba Sarkin ya fara yin ta, kuma ni ne mutum na farko da aka yi wa wannan sarauta. Ina zaton duk masarautun da suke kasar Hausa babu wata masarauta da take da Magawata, ni ne mutum na farko da aka nada hakimi mai wannan sarauta.
Sarautar Magawata sarauta ce da take da daraja, saboda dangantakar sarautar da addini.
Me ya sa aka nada ka Magawata?
Mai martaba ya nada ni Magawata ne sanadiyyar ganin wata da na yi a lokacin duban watan azumi a shekarar 2018 daga nan ne, sai Mai martaba Sarkin Dutse ya rika kira na da Magawata. Ka san komai yana da sila daga nan ne Mai martaba ya nada ni Magawatan na sosai a matsayin hakimi marar kasa
Kana nufin sarauta taka ba ta da kasa?
Hakimi ne ni marar kasa, amma tana da daraja a fadarmu saboda dangantakar al’amarin da Musulunci domin Mai martaba Sarki mutum ne mai kishin addini mai son ci gaban addini yana kokari wajen yada addinin Allah da fadakar da al’umma.
Mene ne aikinka a fada?
Aikina aiki kamar na sauran hakimai marasa kasa ne tunda ni ba na bai wa talaka umarni. Aikina shi ne idan lokaci ya yi aka aiko wa Mai martaba Sarki daga fadar Mai alfarma Sarkin Musulmi a duba wata, ni kuma Mai martaba zai ba ni umarni daga nan ni kuma zan shiga rediyo da jaridu in sanar da jama’a da daukacin hakimai da dagatai da masu unguwanni cewa a fara duban wata kuma da an gani a sanar da hukuma mafi kusa ma’ana a fara sanar da mai unguwa shi kuma ya sanar da dagaci shi kuma ya sanar da hakimi shi kuma zai sanar da ni ni kuma zan sanar da ’yan Kwamatin Shura daga nan za a kira wadanda suka gani a yi musu tambayoyi idan an gamsu da bayanansu sai Mai martaba ya ba da damar a sanar a dauki azumi ko kuma a yi Sallah idan lokacin azumi ya zo karshe.
Fadarka tana yi wa wadanda suka kawo wargi a kan ganin wata hukunci?
Ba a taba samu ba tunda na fara domin duk wadanda suke zuwa suke bayani za ka ga mutane ne sahihai masu kamala ba su da wata matsala da za a ce ba a gamsu da bayanansu ba.
Mene ne sakonka ga al’ummar Masarautar Dutse?
Sakona shi ne ina godiya ga Mai martaba Sarkin Dutse da fadarsa da ’yan majalisarsa da hakimansa. Kuma ina kira ga al’ummar Masarautar Dutse su ba ni hadinkai a duk lokacin da aka ga wata a lokacin azumi da lokacin Sallah saboda in sanar da masarauta.