Dalilin tsadar dauko mawakan Kannywood a bukukuwa
Mutane da dama, musamman masoya mawaqan Kannywood na zamani, na kokawa kan yadda gayyatar shahararrun mawaqan Kannywood don halartar wajen bukukuwa da tarukan siyasa ke da tsada sosai.
Mutane da dama, musamman masoya mawakan Kannywood na zamani, na kokawa kan yadda gayyatar shahararrun mawakan Kannywood don halartar wajen bukukuwa da tarukan siyasa ke da tsada sosai.
Yayin da jama’a ke ganin matakan da shahararrun mawakan ke sa wa kafin a gan su, inda galibi sai an bi ta hannun manajojinsu ko sakatarorinsu ko kuma a bukaci biyan wasu kudi na kafin alkali, wasu kuma na danganta rashin halartar gayyatar da ake wa shahararrun mawakan zuwa bukukuwa da girman kai da kuma rashin kishin masoyansu.
Sai dai a tattaunawar Aminiya ta yi da shahararrun mawakan Kannywood, Alhaji Aminu Ladan da aka fi sani da Alan waka da kuma Mudansiru Kasim dukkansu sun bayyana cewa, wannan zato da kuma kallo da ake wa shahararrun mawakan ba gaskiya ba ne.
Kukan dadi ‘yan Arewa ke yi-Alan waka
Alhaji Aminu Ladan, wanda shi ne Sarkin Adabin kasar Hausa ya ce, duba da yadda shahararrun mawaka a Kudancin Nijeriya da ma fadin duniya suke da matukar tsada wajen gayyatowa da kuma irin tanade-tanaden da ake yi kafin a gayyace su zuwa wajen wani taro, to za a iya cewa, masu fadin cewa, shahararrun mawakan Kannywood na da tsada wajen gayyatowa kawai kukan dadi suke yi.
“Ko a nan Nijeriya idan Ka dubi irin kudin da ake ajiyewa a kasa ba labari ba kafin a gayyato shahararrun mawakan Kudancin kasar nan na Nollywood kamar irin su Davido da Burna Boy da Flavour da Wizkid da sauransu, za ka ga ashe kukan dadi ne ‘yan Arewa ke yi kan cewa, gayyatar mu na da tsada.”
Ya kara da cewa, “misalin da kowa zai iya ganewa shi ne, kwanakin baya an gayyato shahararren mawaki Davido, inda ya zo nan Kano. Kowa ya ji cewa, sai da aka biya shi fiye da Naira miliyan 800. Ka fada min duk a cikin shahararrun mawakan Kannywood wane ne ake biya ko da miliya 200 kafin a gayyace shi?”
Ala ya kuma kara da cewa, “kuma da ya zo Kano budurwarsa ya wake ba wata sabuwar waka ya yi wa wadanda suka gayyato shin ba. Savanin mu mawakan Kannywood, wanda idan mutum ya gayyace ka zuwa taron biki sai ka zauna, ka vata lokacinka da tunaninka, ka yi masa sabuwar waka da har ‘yan uwansa da abokaninsa sai la ambata a ciki. Amma duk da haka yana kyashin ba ka Naira miliyan biyar da ka caje shi. Duk kuwa da yake ko a wajen taron watakila sai ka sanya sabon dinki da sababbin takalma da sabuwar hula ban da kudin dawainiya mota naka da na yaranka.”
Da ya juya wajen yadda al’umma ke girmama mawaka a Kudu, Sarkin Adabin Hausa ya ce, “har yanzu kima da tagomashin da mawaka a suke samu a Kudu ya ninka wanda ake ba wa mawakan Kannywood, ganin yadda a Kudu ake girmama mawaka tare da ba su matsayi a siyasance, ta yadda kowa ke alfaharin kasancewa yana da dangantaka da su.
“Mu fa har yanzu a Arewa kallon maroka ake mana, saboda a al’ada ana ganin mawaki a matsayin maroki. Koda aure ka nema sai wani ya kai suka kan cewa, kada a ba wa maroki mata. Alhali mu kuwa ba maroka ba ne, sana’a ce muka sanya jarinmu da basirarmu.
Muna kama hayar ofisoshi ,musamman a Titin Hanyar Gidan Zu da ke Kano, inda babu shagon da ake biyan hayarsa kasa da miliyan biyu da rabi. Sannan mu dauki ma’aikata kama daga sakatarori zuwa manajoji da muke biya albashi duk wata.”
Ala wanda kuma shi ne danburan din Sarkin Gobir, daga karshe ya shawarci masoyansu da su rinka daukar mawaka da kima tare kuma da daukar matakin daidai ruwa daidai tsaki a duk yayin da suka tashi gayyato mawaki zuwa wajen wani taro ko biki.
Kowane mawaki da tagomashinsa yake tafiya-Mudassiru Kassim
Shi ma Mudassir Kassim, wanda fitaccen mawakin Hausa ne a Masana’antar Kannywood, inda ya fara waka a masana’antar tun daga shekarar 1998.
A zantawarsa da Aminiya dangane da yadda ake ganin ana kashe kudi tsababa wajen gayyatar shahararrun mawakan Kannywood, don su halarci taruka ko bukukuwa a Nijeriya da ma sauran sassan duniya, inda ya bayyana cewa, kowane mawaki da tagomashinsa yake tafiya.
Kana kuma shahara ko tashen da tauraruwar mawaki ke yi na daya daga cikin dalilan da suke taka rawa wajen tsadar dauko shi a wajen biki.
Ya kuma bayyana cewa, shi yakan je inda duk ta kama ya je aiki shi da yaransa idan an gayya ce shi.
Ya kara da cewa, ya danganta da a ina ake son ya je, wanda hakan ke fayyace ko a mota ko a jirgin sama ne ta kama ya yi tafiyar.
Mudassir Kassim ya bayyana cewa, yana daya daga cikin manyan mawakan Kannywood da aka fara gayyata zuwa wasu birane tun a shekarun baya, don nishadantar da taruka da bukukuwa na al’ada. Ya kuma bayyana cewa, waka a wurinsa kasuwanci ne.
Ya ce, shi kafin a gayyace shi zuwa irin wadannan bukuwan akwai tanade-tanade da ake yi masa da tawagarsa na masauki da abinci da kuma da sauran wasu dawainiyoyin da aka yi yarjejeniya.
“Ya danganta ne da irin taron da kuma yarjejeniyar da kuka yi da mai son daukar ka. Akwai wanda zai so ka hada masa komai, tun daga kan kudin mota da na abinci da na wurin zamanka da yaranka. Kai har ma yarjejeniya a kan in an yi liki, wani zai ce, zai biya ka kaza, amma babu ruwanka da kudin da za a lika, wani kuwa babu ruwansa da kudin da za a lika.
Haka kuma wajen kudin sufuri ,wanda ya danganta da inda za ka je, idan wuri mai nisa ne, sai an biya mana kudin jirgi. In kuwa babu nisa sosai, muna zuwa a mota ne kuma wanda ya gayyace mu ke biyan dawainiyar motocin.”
Nakan bayar da zavin sayen tikitin jirgin sama ko shatar mota-Maryam A. Sadik
A tattaunawa da ta yi da Aminiya, Maryam A. Sadik, wacce ta fara waka tun a shekarar 2017, ta ce, ta fara wakokin biki da siyasa ne har ta samu daukaka. Ta kuma bayyana cewa, idan za ka dauke ta, je ta yi waka zuwa wani biki ko taro da farko kamar sauran manyan mawaka a kan samu manajanta ne, wanda shi ne zai tattauna a kan ko wane irin aiki ne ake son ta yi.
Ta bayyana cewa, idan ana so ne ta yi waka sabuwa to irin cajin da za a yi wa mutum daban ne. Haka kuma idan sabuwar wakar ma na bukatar yin amfani da ’yan amshi ne ita ma akwai irin cajin da za a yi wa mai so a yi masa waka.
“ A gaskiya ina da manaja da za ka je, ka samu, shi za ku yi magana komai da komai. Idan farashin iya waka da ni daya zan yi ta ko kuma kuma har da yara na zan je a yi ta, farashin daban ne.
‘’Ka ga idan zan bar uzurina, in zauna, in shirya maka wak,a farashin ne mai zaman kansa. Idan kuma iya zuwa kake so, in yi, ba tare da na yi wata sabuwar wakar ba, kawai dai kana son, na zo, in yi wakokin soyayya da aka san ni da su, shi ma farashinsa daban yake,” in jita.
Game da tsarin yadda take yin tafiye-tafiyenta idan an gayyace ta kuwa sai ta ce, “misali idan kamar a irin su Abuja ne, ina bai wa mutum zavi biyu ne ko ya saya min tikirin jirgin sama tare da yarana ko kuma in dauki shatar mota.”
l