Dalilinmu na ilimantar da nakasassu – Sangie

Shugaban makarantar Sunnah Pribate School da ke Unguwar Rimi a garin Jos, Jihar Filato Malam Idris Abdullahi Sangie ya ce sun bude sashin koyar da nakasassu a makarantar ne don su taimaka wa nakasassun su iya karatu da rubutu kyauta, ta yadda in sun kammala za su iya yin aikin gwamnati da sauransu kamar yadda […]

Dalilinmu na ilimantar da nakasassu – Sangie

Malam Idris Abdullahi SangieShugaban makarantar Sunnah Pribate School da ke Unguwar Rimi a garin Jos, Jihar Filato Malam Idris Abdullahi Sangie ya ce sun bude sashin koyar da nakasassu a makarantar ne don su taimaka wa nakasassun su iya karatu da rubutu kyauta, ta yadda in sun kammala za su iya yin aikin gwamnati da sauransu kamar yadda sauran jama’a ke yi.

Malam Idris Abdullahi Sangie ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce da farko suna karantar da yara ne da ba su da matsala. Sai suka lura cewa al’umma na barin yaran da suke da nakasa ba sa lura da su, suna barinsu suna yawon bara.
Malam Idris Sangie ya ce sun fara bude sashin nakasassu ne da guragu ne, inda suka rika dauko yara guragu suna koyar da su kyauta. “Da muka ga irin nasarar da muke samu, sai muka hada da kurame da masu nakasar hankali, babu shakka sun samu nasarori, domin a cikin guragun da muke koyarwa akwai yarinyar da take aji biyu na babbar sakandare da take daukar na daya ko na biyu, kuma a cikin guragun akwai yarinyar da take rubuta komai da kafa,” inji shi.