Dalilinmu na yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi – Salisu Hamza Maigemu

Kungiyar Gizago ta karrama ka, ko za ka yi karin bayani kan wannan? Alhamdu lillahi, kungiyar Gizago na dade a tare da ita, kusan akalla shekara uku ke nan ko hudu ina halartar tarurrukanta, musamman lura da manufofinta na alheri da yadda suke zumunci da yada wasu abubuwa na alheri. Shi ya sanya na zama […]

Dalilinmu na yaki da tu’ammali da miyagun kwayoyi – Salisu Hamza Maigemu

Kungiyar Gizago ta karrama ka, ko za ka yi karin bayani kan wannan?

Alhamdu lillahi, kungiyar Gizago na dade a tare da ita, kusan akalla shekara uku ke nan ko hudu ina halartar tarurrukanta, musamman lura da manufofinta na alheri da yadda suke zumunci da yada wasu abubuwa na alheri. Shi ya sanya na zama daya daga cikin mambobinta; daga karshe ma har suka ba ni matsayin daya daga cikin iyayenta a nan Jihar Katsina. To, ina ganin shi ya sanya a yau suka karrama ni saboda gamsuwa da abubuwan da muke yi, suka ga na cancanta su karrama ni.

daya daga maudu’in da aka gabatar a taron nan shi ne illolin tu’amali da kwaya da kayan maye a cikin al’umma. A matsayinka na daya daga cikin shugabannin al’umma, me za ka ce kan illar tu’ammali da kwaya?

To, alhamdu lillahi, ita kwaya da shanta da fataucinta ba karamin ta’addanci ba ne ga dan Adam a cikin kasa, domin duk wasu abubuwan barna da za a gani a cikin kasa, irin su sace-sace da ta’addanci da rashin ji da daukar magana da karya tattalin arziki, duk suna da alaka da sha da fataucin miyagun kwayoyi. To gaskiya wannan ba abin alheri ba ne kuma muna kira ga al’umma su guje shi. Wannan taro ya yi mini dadi, domin kamar yadda Bahaushe ya ce, kowa ya je yaki sarki ya taya. Mu da muke cikin gwamnati, babu abin da muke yi sai ganin cewa an daina tu’ammali da miyagun kwayoyi, ni kaina a matsayin dan majalisa a makonni biyu da suka gabata, na tara matasa sama da 250, inda na gayyato masana da jami’an Hukumar Hana Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ’yan sanda da SSS da ’yan banga, inda muka yi musu nasiha, muka nuna masu illoli shaye-shaye a matsayinsu na matasa. Kuma mu a matsayinmu na shugabanni, ba mu goyon bayan haka. Yanzu siyasa ta girma, ba abu ne na iface-iface da satar akwati, ko ka tsorata mutane ko a bugi wani ba. Siyasa ce ta zahirin abin da mutane ke bukata da wanda suke bukata ya shugabance su.

Wadansu na dora laifi kan ’yan siyasa, cewa su ne ke ingiza matasa ga shaye-shaye domin cimma bukatunsu na siyasa, me za ka ce?

To ni kuma ta bangarena na fi zargin ’yan jarida da malamai. Dalili shi ne, duk abin da za ka fadi ka fadi gaskiya, komai ta ja maka ka biya. Kullum, ba ka yi wa mutane kudin goro, akwai mutumin da za ka ga cewa ba ya goyon bayan irin wannan. Don haka idan ka dora laifin ga ’yan siyasa, kamar ka ce dukansu ke nan. Yana da kyau ga ku ’yan jarida da malamai masu hawa mumbari su rika fadakar da mutane cewa akwai mutane nagari, su rika kwatance da mutanen kirki, wadanda suka dauki matakan ganin bayan tu’ammali da miyagun kwayoyi. Kamar yadda na fada maka, idan za ka ce ’yan siyasa, ni ina cikinsu, to amma wallahi tallahi, idan kana so raina ya baci, to in ga mutumin da bai san ciwon kansa ba. Ma’ana, in ga wanda ke safarar kwayoyi ko sha ko wanda ke bangar siyasa. Da na gamu da irin wadannan sai raina ya rika baci. Ni dan siyasa ne, don haka ba na goyon bayan mai sha kuma ba na sha kuma ina cikin siyasar nan ta adawa tun shekara goma sha a baya. Idan ka lura, a da ba ma zaben ake ba, irin wadannan ’yan banga ke korar mutane su sace akwatuna su dangwale. Yanzu kuwa abin da ake so ga dan siyasa, ya jawo mutane, a kada kuri’a, a kirga gaban kowa, domin a duk lokacin da ka jawo ’yan banga a siyasarka, to kamar korar mutane kake yi. Shi mutumin kirki, idan ya gan ka da ’yan banga, bai ma zuwa inda kake.

Jam’iyyarku ta APC a Jihar Katsina, ta zabi amfani da tsarin wakilai wajen fitar da gwanaye maimakon tsarin ’yan tinke, me za ka ce?

Abin da ke faruwa shi ne, wadansu mutane ba su san illar da ke tattare da gudanar da zaben ’yar tinke ba. Mu da muke cikin APC, mun shiga zabe a 2011, inda muka fitar da ’yan takararmu ta hanyar ’yar tinke, wanda idan za ka bincike tarihi a Jihar Katsina, zabubbuka uku aka yi amma babu sahihi ko daya, domin duk wanda ya samu dama kayan zabe suka fada hannunsa, shi ke nan; duk layin nan da kake gani, layin iska ne. Kuma wadanda suke ganin ba su da jama’a, za su zo wajen tarurrukan nan su ta da hankali, karshe a kashe mutane. Kuma idan ka kula, akwai karancin jami’an tsaro a ko’ina, muna da mazabu 361 a Jihar Katsina, muna da rumfunan zabe sama da dubu 40, ta yaya za ka wadata su da jami’an tsaron da za su kula da su a wanye lafiya?

Don haka ba son rai ne ya sa aka zabi wannan tsari ba, an yi haka ne domin tsabtace tsarin, kuma a Jihar Katsina, duk da cewa an zabi tsarin wakilai a zabe, babu wanda Mai girma Gwamna ya ce a goyi bayansa, an bar mu da wakilai, su kuma su za su zama wakilan jama’a a kowace rumfa da mazaba, su tabbatar da cewa amana ce ta mutanenmu, su kalli mutanensu. Babu wanda zai yi musu barazana ko ban tsoro.

An yi zaben Sanata na cike gurbi a Shiyyar Daura kwanakin baya, an yi zaben dan Majalisar Tarayya na Mashi-Dutsi, kowa ya ga yadda aka gudanar da shi, ba wanda ka yi wa barazana, babu kuma wanda za a raba da mukaminsa, don ya zo ya zabi abin da yake ra’ayi a matsayinsa na wakili.

A matsayinka na dan majalisa, ko za a iya cewa kwalliya ta biya kudin sabulu a mazabarka?

Ni abin da ya sa zan ce kwalliya ta biya kudin sabulai ma ba sabulu ba shi ne, lura da inda na fito. Ni ina wakilicin karamar hukuma daya ce daga cikin 34 a jihata ta Katsina, wato Kankiya ke nan. Idan ka kalli wannan karamar hukuma a shekara ukun nan da muka yi, ina da ayyuka da gwamnatin jiha ta yi na sama da Naira biliyan hudu zuwa biyar, wadanda kuru-kuru ga su nan kowa na gani, talakan da ke wurin da kowa da kowa ya san an yi. Sabanin waccan shekara 16 da ta gabata, wallahi babu wani mutum guda a Kankiya da zai iya nuna maka aikin Naira biliyan biyu, duk da yake sun samu kudi ninkin abin da ake samu a yanzu. Don haka za mu ce kwalliya ta biya kudin sabulu.