Dam Ɗin Ɗanbatta Ya Ci Ɗaliban Kwaleji
Rahotanni daga jihar Kano na tabbatar da hallakar wasu ɗalibai biyu na kwalejin koyon aikin gona ta Audu Bako da ke kusa da garin Danbatta. Ɗaliban sun mutu ne bayan kwalekwalen da suka shiga ya kife a tsakiyar dam din Thomas da ke Karamar Hukumar Makoda a jihar. An ce masu kawo ɗauki sun yi […]
Rahotanni daga jihar Kano na tabbatar da hallakar wasu ɗalibai biyu na kwalejin koyon aikin gona ta Audu Bako da ke kusa da garin Danbatta.
Ɗaliban sun mutu ne bayan kwalekwalen da suka shiga ya kife a tsakiyar dam din Thomas da ke Karamar Hukumar Makoda a jihar.
An ce masu kawo ɗauki sun yi nasarar ceto ɗaya daga cikin daliban, yayin da ake ci gaba da neman sauran.
Jami’in yada labarai na karamar hukumar Makoda Sani Muhammadu ya tabbatar da cewa lamarin ya faru ne da safiyar Talata a lokacin da daliban ke hanyarsu ta komawa kwalejin.
Sani ya ce, an yi nasarar gano gawar daya daga cikin daliban mai suna Abubakar Sanusi, ya bada tabbacin cewa za a cigaba da laluben sauran daliban.
Ya bayyana cewa cikin ikon Allah direban kwalekwalen ya tsallake rijiya da baya a hatsarin.
Wani mazaunin Danbatta Abba Muhammad ya jaddada bayanan jami’in yada labaran, inda ya kara da cewa dalibin da aka ceto yana karbar magani a babban asibitin Danbatta.