Damar tserewa daga Najeriya nake nema —Buhari

Tsohon shugaban ya ce ya yi abin da zai iya kuma ya bar ’yan Najeriya su yi alkalanci.

Damar tserewa daga Najeriya nake nema —Buhari

buhari

Tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya ce ba don rufe iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar da aka yi ba, da tuni ya bar Najeriya ya san inda dare ya yi masa.

A hirarsa ta farko tun bayan saukarsa daga mulki, Burahi ya shaida wa gidan talabijin na kasa (NTA), cewa duk da cewa ba shi ba ne sugaban kasa, har yanzu mutane ba su bar shi ya huta ba, inda kullum suke zuwa suna takura masa.

Buhari wanda ya mika mulki ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu Mulki a ranar 29 ga watan Mayu, ya ce ya yi iya kokarinsa a cikin a mulkin da ya yi.

Ya kara da cewa ’yan kasar suna da wuyar sha’ani wanda hakan ya sa shugabantar su ke da wahalar gaske, amma duk da haka, ya yi iya kokarinsa.

“Allah ya ba ni damar yi wa kasata hidima, kuma na yi iya kokarina. Amma ko abin da na yi ya wadatar, wannan kuma na bar mutane su yi hukunci.

“’Yan Najeriya suna da matukar wuyar sha’ani. Mutane sun san abin da ya kamata su aikata, amma sai su ki, saboda suna ganin sun fi wanda ke shugabantar su sanin abin da ya dace.

“Sun san hakkokinsu kuma suna ganin su suka fi dacewa da kujerar ba wanda ke kai ba, don haka, suna sanya ido a kan duk abin da kake yi.

“Saboda haka kai kuma kullun kokarinka shi ne gwagwarmaya ba dare ba rana don ganin ka yi yadda suke so,” in ji shi.

Da aka tambaye shi game da nagartar mukarraban gwamnatinsa ta shekara takwas, Buhari ya mayar da martani da cewa “wannan matsalarsu ce.”.

Ya kara da cewa ya kamata masu sukar gwamnatinsa su yi wa kansu tambaya kan rawayar da kowannensu ya taka a wajen yakar cin hanci da rashawa.

Buhari ya bayyana cewa ya nada mutane kuma ya ba su damar gudanar da ayyukansu a lokacin da ya ba su ayyuka, yana mai jaddada cewa idan da za a sake ba shi dama, ba zai yi wani abu daban ba a tsarin Najeriya a yanzu.

Dalilin sauya fasalin kudi

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya amince da sauya fasalin takardun naira ne don kare mutuncinsa da kuma tabbatar wa ’yan kasa cewa babu barauniyar hanyar da mutum zai bi domin kaiwa ga nasara a zabe.

“Ko ’yan Najeriya sun yarda ko ba su yarda ba, mu kasa ce da ba ta ci gaba ba. Kuma a irin wannan yanayi, akwai wadanda ba su damu da yadda suka tara kudi ba.

“Har yanzu ina jin cewa hanya daya tilo da zan iya hana wadannan mutane ita ce kawai in tabbatar da nagartata… Ina ganin a matsayin kasa mai tasowa har yanzu muna da sauran aiki a gabanmu.

“Dalilin da ya sa shi ne don nuna wa ’yan Najeriya cewar babu wata barauniyar hanyar da za a bi wajen samun nasarar jagoranci,” in ji shi.