Dambarwar da ta biyo biyo bayan kyautar Ballon d’Or
Rodri shi ne ɗan wasa na farko a tarihin ƙungiyar da ya lashe kyautar Ballon d’Or.
Tun gabanin ayyana ɗan wasan tsakiya na Manchester City da Spain, Rodri a matsayin wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta kakar 2023/24, aka yi ta samun ka-ce-na-ce kan ainihin ɗan wasan da ya cancanta da zama gwani-na-gwanaye.
Ɗan wasan mai shekaru 28, wanda ya yi rashin nasara a wasa ɗaya kacal a kakar wasan da ta gabata a kulob ɗin da kuma ƙasarsa, an ba shi kyautar ne a birnin Paris bayan ya taimaka wa Spain ta lashe gasar Euro 2024 a watan Yuli.
Ya kuma lashe gasar Premier da Uefa Super Cup da kuma gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi tare da City.
Rodri shi ne ɗan wasa na farko a tarihin ƙungiyar da ya lashe kyautar Ballon d’Or.
Sai dai bikin za a cewa ya bar baya da ƙura, sakamakom yadda Rodri ya doke ɗan wasan Real Madrid ɗan asalin Brazil, Ɓinicius Junior.
Bayan gaza lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon ƙafan ta duniya Ɓinicius Junior ya ɗora alhakin rashin nasararsa kan yaƙi da yake yi kan wariyar launin fata a fagen wasanni.
A yanzu dai rahotanni na cewa Ɓinicius ya yi amanna da cewa rashin nasararsa tana da alaƙa da fafutukarsa kan kawar da wariyar launin fata daga harkar wasanni.
An shammaci Real Madrid da Ɓinicius da ma masoyansu cike da al’ajabi a daren Litinin, bayan da ta bayyana cewa Ɓinicisu bai lashe kyautar ba, duk da nasarorin da ya samu na lashe gasannin La Liga da Zakarun Turai.
Wannan ya haifar da tawagar Madrid ta ƙaurace wa bikin ba da kyautar a birnin Paris, inda aka karrama Rodri da babbar kyautar bajinta a ƙwallo ɓangaren maza.
Zuwa yanzu, Ɓinicius Jr ya bayyana matsayarsa game da gaza lashe kyautar, cikin wani saƙo da ya wallafa a soshiyal midiya, inda ya ce a shafinsa na X cewa: “Zan sake yin bajinta ninki 10 idan haka ake so na yi. Ba su shirya ba.”
Fafutukar kare baƙaƙe
A wani lokaci a Maris, Ɓinicius ya fashe da kuka lokacin da aka tambaye shi game da zagin launin fata da ake yawan yi masa a yayin wasanni, wanda ake ganin ya kusa kassara ƙarfin zuciyarsa.
Ɓinicius ya taɓa yin kiran da a karɓe damar karɓar baƙuncin gasar Kofin Duniya ta 2030 daga wajen Sifaniya, idan zagin launin fata ya ci gaba da faruwa a ƙasar, kuma ya nemi a riƙa tura masu nuna wariyar launin fata zuwa kurkuku kai-tsaye.
Haka nan, Ɓini ya yi suna wajen nuna goyon baya ga ’yan wasan da suka fuskanci zagin launin fata, kamar Raphinha da Lamine Yamal da Alejandro Balde na Barcelona, waɗanda suka sha zagi yayin wasan El Clasico da aka yi a makon jiya a gidan Real Madrid.
Jami’an da ke kula da Ɓini sun faɗa wa Reuters cewa ɗan wasan yana magana ne kan yaƙin da yake kan wariyar launin fata, lokacin da ya yi magana kan zaɓen Ballon d’Or.
Tawagarsa ta ce: “Duniyar ƙwallo ba ta shirya karɓar ɗan wasa da ke faɗa da tsarinsu ba.”