Dambarwar Jihar Filato: Duk wanda ya ki dawo da kudin jama’a doka za ta hukunta shi – Barista Hawaja
A tsakiyar wannan wata ne kwamitin da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya kafa a karkashin jagorancin Mataimakinsa Farfesa Sonni Tyoden don binciko yadda tsohuwar gwamnatin Jonah Jang ta yi da kudaden da aka ba ta a cikin shekara takwas na mulkinta a jihar, ya mika rahotonsa. Rahoton ya ce gwamnatin Jang ta samu Naira […]
A tsakiyar wannan wata ne kwamitin da Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya kafa a karkashin jagorancin Mataimakinsa Farfesa Sonni Tyoden don binciko yadda tsohuwar gwamnatin Jonah Jang ta yi da kudaden da aka ba ta a cikin shekara takwas na mulkinta a jihar, ya mika rahotonsa. Rahoton ya ce gwamnatin Jang ta samu Naira biliyan 525 da miliyan350 a shekarun, kuma ta yi almundahana tare da bar wa jihar bashin Naira biliyan 222 da miliyan 300. Rahoton ya tayar da kura a tsakanin jami’an tsohuwar gwamnatin da gwamnati mai ci. Kan haka ne wakilinmu ya tattauna da Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Barista Yusuf Gambo Hawaja da tsohon Mai taimaka wa Jonah Jang kan Harkokin Watsa Labarai Mista Pam Ayuba:
Aminiya: A kwanakin baya Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya karbi rahoton kwamitin binciken yadda tsohuwar gwamnatin jihar ta gudanar da mulkin jihar, mene ne makasudin kafa kwamitin?
Barista Hawaja: Ganin yadda aka yi abubuwan da ba su kamata a zamanin gwamnatin da ta gabata ba kuma ba za a dauki hukunci haka kawai ba tare da bincike ba, ya sanya wannan gwamnati ta kafa kwamitin a karkashin Mataimakin Gwamna Farfesa Sonni Gwanle Tyoden, don ya binciko zargin gaskiya ne ko ba gaskiya ba. Kwamitin ya yi bincikensa ya kawo wa Mai girma Gwamna Simon Lalong kuma gwamnatin jihar za ta yi nazarin rahoton kwamitin.
Aminiya: Kamar wadanne abubuwa ne rahoton kwamiti ya gano?
Barista Hawaja: Rahoton kwamiti yana magana ne kan bayanan kudaden da aka ba gwamnatin da ta gabata, tun daga lokacin da suka hau mulki a shekarar 2007 zuwa bana da ta sauka. Domin wannan gwamnati ta san abin da ta tarar, kuma ta san abin za ta dora a kai. Saboda idan aka bar wannan abu a haka ya zama an yi kitso da kwarkwata ke nan. Nan gaba idan wani abu ya faru, zai zama ba mu da hujjar da zamu kare kanmu. Don haka dole ne mu san abubuwan da suka faru a tsohuwar gwamnatin, mu ma idan muka tafi muna son a yi mana haka, a ga abin da muka yi gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne, wannan shi ne adalci.
Aminiya: To, kamar wane irin mataki za ku dauka kan mutanen da ake zargin sun yi almundahanar kudaden jihar a cikin rahoton kwamitin?
Barista Hawaja: Sai gwamnati ta yi nazari kafin ta san matakin da za ta dauka kan mutanen da ake zargi da almundahanar kudaden jihar a zamanin gwamnatin da ta gabata. Domin akwai dokokin kasa da suka tanadi hukunce-hukunce, da idan aka yi wani abu da bai kamata ba doka za ta yi aikinta. Don haka ba ma yin gaggawa don kada mu yi abin da bai kamata ba. Amma Gwamna ya ce idan mutum ya san da wani abu na gwamnati a hannunsa, ya gaggauta dawowa da abin kafin a ce za a kwato.
Mutum ya kawo a asirce ya nuna wa gwamnati nadamarsa shi ke nan, amma idan ya ja daga, sai doka ta yi aikinta. Don haka duk wanda ya kwashi kudin al’ummar Jihar Filato ya dawo da su, saboda a yi ayyukan da suka kamata. Idan mutum ya ki har makon biyun da Gwamna ya diba suka cika sai doka ta yi aikinta.
Aminiya: To, amma jami’an tsohuwar gwamnatin sun musanta zarge-zargen almundahanar da ake yi musu, me za ka ce?
Barista Hawaja: Dama yawanci duk mutanen da ake tuhuma da laifi, sukan musanta sun aikata laifin da ake tuhumarsu, don haka bincike ne yake tabbatar da cewa an yi laifi ko ba a yi ba. Wannan ba wani abu ne sabo ba, kuma irin wannan bincike yawanci ba ya da damuwa domin abu ne na takardu. Akwai hanyar da kudade suka shiga a rubuce, akwai hanyar da suka fita a rubuce. Idan aka ba ka kudi kai ne za ka yi bayanin yadda ka yi da su.
Aminiya: Wane sako kake da shi ga al’ummar Filato kan wannan al’amari?
Barista Hawaja: To, sakona al’ummar Jihar Filato shi ne su bai wa gwamnatin da suka zaba goyon baya da hadin kai. Mu hada hannu mu ciyar da jihar nan gaba. Su kuma jami’an tsohuwar gwamnatin sun yi zamaninsu, abin da yake hannunsu na gwamnati su dawo da shi, domin a yi wa jama’a aiki. Wannan sabuwar gwamnati ba ta zo ne don ramuwar gayya ba.