Dambarwar majalisa: Dole ne a bi umarnin jam’iyya —Balarabe Musa
Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa shi ne tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PRP a Jamhuriyya ta Farko, kuma yana daga cikin gwamnonin da suka bijire wa jam’iyyarsu a wancan lokaci. Sai dai a zantawarsa da Aminiya a kan rikicin da ke faruwa a tsakanin Jam’iyyar APC da shugabannin Majalisar Dokoki ya ce tilas […]

Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa shi ne tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Kaduna a karkashin Jam’iyyar PRP a Jamhuriyya ta Farko, kuma yana daga cikin gwamnonin da suka bijire wa jam’iyyarsu a wancan lokaci. Sai dai a zantawarsa da Aminiya a kan rikicin da ke faruwa a tsakanin Jam’iyyar APC da shugabannin Majalisar Dokoki ya ce tilas ne ’yan majalisa ko ’ya’yan jam’iyya su rika yin biyayya ga jam’iyyarsu domin a karkashinta suka samu aka zabe su
Aminiya: Mene ne ra’ayinka a kan dambarwar da ke faruwa a Majalisa Dokoki ta kasa, musamman Majalisar Dattawa?
Balarabe Musa: Ina kallon wannan abu ne a matsayin gwagwarmaya a tsakanin jam’iyya da zababbun wakilai, ita Jam’iyyar APC tana ganin ita ta ba da sunan dan majalisa ya zama dan majalisa domin ya je ya wakilci jam’iyya a majalisar. Shi ma dan majalisa ya yarda hakan ne, amma yana cewa ba zai yarda jam’iyya ta tursasa shi ba. Yana son ganin ya yi abin da yake ganin ya kamata a majalisa.
Kuma su zabe wadanda suke ganin ya kamata su zaba rigimar ke nan tsakanin jam’iyya da dan jam’iyya wanda jam’iyya ta ba da sunansa ya kuma ci zabe.
Aminiya: Kana ganin ya dace yadda shi Shugaban Majalisar Dattawa da aka zaba ya ki bin umarnin jam’iyyarsa?
Balarabe Musa: Ko kadan bai dace ba, kuma idan aka ci gaba da yin haka ke nan babu amfanin jam’iyya. Maimakon jam’iyya wadda ita ce aka yi wa rajista a kan wata manufa wadda ta bayar kuma a kanta aka yi mata rajista, kuma jam’iyya ita ta ajiye dan takara wanda da ba don ta ajiye shi ba, babu yadda za a yi ya zama dan takara har ya ci zabe, ba don ta ajiye shi ba babu yadda za a yi ya zama dan majalisa. Saboda haka tilas ya saurari jam’iyyarsa in ko bai saurari jam’iyyarsa ba, ba ya da gaskiya. Kuma dole jam’iyya ta bi duk yadda za ta bi domin tilasta duk dan majalisar da bai saurare ta ba. Kuma idan har dan majalisa ba zai saurari jam’iyyarsa ba ke nan jam’iyyar ba ta da amfani.
Aminiya: Wasu na ganin ita kanta jam’iyyar bai kamata ta yi shisshigi a harkokin majalisa ba kasancewar majalisa tana cin gashin kanta ne. Me za ka ce a nan?
Balarabe Musa: Ai ba shisshigi ba ne domin kamar yadda na ce ne ita jam’iyya ita ta tsayar da shi ba don ta tsayar da shi zabe ba ai bai ci zaben ba. Kuma an tsayar da shi ne domin ya wakilci jam’iyya a majalisa ba wai ya wakilci kansa ba. An san cewa idan ka aika mutum ya je ya yi maka wani aiki ya dace ka dan ba shi dama domin ya yi maka wannan aiki yadda ya kamata. An san da haka, amma kada ka yarda ka wuce gona da wuri domin mai yiwuwa ne ita jam’iyya akwai abin da take hanga wanda kai ba za ka iya hangowa ba.
Aminiya: Amma kai ma a lokacinku kun fuskanci irin wannan matsala inda kuka ki bin umarnin jam’iyyarku ta PRP har ta kai ga an rabu aka samu ’yan tsansi da ’yan tabo. Me ya sa ka canja ra’ayi a kan haka?
Balarabe Musa: Babu shakka akwai bambanci, domin mu a lokacinmu abin da ya kawo rigimar cewa ake a yi kawance da NPN, mu kuma muka ga idan aka yi wannan kawance da NPN din nan ma’anar PRP ya tashi ke nan zai zama babu ma’ana. Na biyu kawance da NPN zai kawo raba Najeriya domin yadda aka fito da kawancen shi ne a yi kawance da PRP da NPN, mu kuma a wancen lokaci muna ganin hakan zai raba Najeriya gida biyu ne tsakanin Arewa da Kudu. Su NPN suna siyasar Arewa, ita kuma PRP na siyasar kasa. Idan aka ce za a yi wannan kawance ke nan za a yi yaki ne tsakanin Kudu da Arewa. Bari in ba ka misali, akwai lokacin da bayan an gama zabe kafin a kafa gwamnati, NPN ta ce tana son a yi gwamnatin hadin gwiwa amma ban da UPN ban da kuma GNPP sai dai a yi PRP da NPN da NPP. In kuwa aka yi haka babu shakka an raba kasar ke nan. Mu kuma sai muka ce a’a ba mu yarda ba, duk kuwa da cewa dai wannan ra’ayin jam’iyya ce gaba daya ba mu rabu a kan haka ba. PRP a karkashin shugabancin Malam (Aminu Kano) ta ce ta yarda a yi gwamnatin hadin gwiwa amma kowace daya daga cikin jam’iyyun nan biyar da yake jam’iyuu biyar ne a lokacin ana yi da ita. Idan kuwa aka ce za a cire jam’iyya daya daga cikin kawancen nan, PRP ba za ta shiga cikin gwamnatin ba haka kuwa aka yi.
Da NPN ta nace ba za ta yi da GNPP da UPN ba, PRP sai ta ce ita ba za ta shiga gwamnatin kawance ba domin za a raba kasa ne kuma ba za a ta domin hadin kan kasa ba ne. Wannan shi ne ya kawo rabuwa a lokacin, sannan akwai wasu abubuwa amma dai wannan shi ne ya kawo rabuwa. Sannan farkon rabuwar shi ne bayan an yi zabe a watan tara (Satumba) ba a ma rantsar da mu ba.
Aka yi taro a kan cewa wadansu manyan ’yan jam’iyya wadanda su ba su ci zabe ba suka fara guna-guni cewa zababbun ’yan jam’iyya kamar Gwamna da ’yan majalisa sun fara maganganu da bai dace ba, a ce wai sun fito daga jam’iyya. Sai aka zo da nufin maganin haka, har aka kafa kwamitin da zai ladabtar da gwamnoni da zababbun ’yan jam’iyya.
A nan ne aka amince cewa Malam Aminu Kano a matsayinsa na shugaban jam’iyya ne kadai zai iya ladabtar da wani dan jam’iyya Gwamna ne ko dan majalisa da ya yi ba daidai ba. Dalili kuwa shi ne shi Gwamna din nan ko dan majalisa ban da dokar jam’iyya akwai dokar kasa wanda shi ke kula da ita. Su shugabannin jam’iyya ba duka ne za su kula da hakan ba.
Amma shi Malam tilas ya kula da hakan kuma idan abu ya baci laifi na kansa ne. Wannan ne ya sa masu hangin nesa suka ce an yarda a ladabtar da zababbu amma shugaban jam’iyya ne kadai zai iya ladabtar da Gwamna, saboda haka komai a shirye yake.
Aminiya: Yaya kake kallon rashin sanya baki na Shugaban kasa Buhari a kan wannan rikici, ya dace ya yi haka?
Balarabe Musa: karshen idan zababbun ’yan majalisa ba su iya daidaitawa ba tilas Shugaban kasa ya sa baki. Domin Shugaban kasa ne ke da alhakin ya ga cewa al’amuran kasa sun daidaita an kuma samu ci gaba, wato a takaice Shugaban kasa ne ’yan kasa ke son ya jagorance su a kai ga ci ba ’yan majalisa ba.
Su ’yan majalisa an zabe su ne su taimaka wa Shugaban kasa ya kai ga cin nasara saboda haka duk da an san cewa akwai buaktar raba aiki tsakanin ’yan majalisa da majalisar zartaswa amma duk da haka Shugaban kasa komai ya baci shi za a duba ba ’yan majalisa ba. Shi ne ke kai kasa ga ci ba ’yan majalisa ba. Yanzu a wannan rigima da ake yi idan Jam’iyyar APC ta gaza shawo kan ’yan majalisa a tafi daidai to, tilas ne Shugaban kasa ya sa baki.
Idan kuma Shugaban kasa bai sa baki ba, abubuwa za su kara lalacewa. Ai irin wannan ya auku a Jamhuriyya ta Biyu lokacinmu. A kan maganar cewa ’yan majalisa su yi doka a kan abin da za a basu na maganar albashi da alawus. Shugaban kasa a lokacin Alhaji Shehu Shagari ya ce a’a bai da ce ku ’yan majalisa ku fadi abin da za a rika ba ku ba a matsayin albashi. Domin za a yi son kai sannan na biyu ya nemi su lura da halin da tattalin arziki ke ciki domin gudun karya tattalin arziki amma suka ki.
Da suka ki yarda da shawarar da ya bayar har ta kai ga Shugaban kasa ya damu, sai wata ran ana taron Majalisar Tattalin Arzikin kasa da gwamnoni da Mataimakin Shugaban kasa da Gwamnan Babban Banki saboda Shugaban kasa ba ya cikin taron, sai ya nemi mu da ’yan majalisar mu halarci taron cin abinci amma ’yan majalisar suka ki saboda kawai ya ki yarda su yi wa kansu albashi.
Aminiya: A takaice wacce shawara za ka bai wa ’yan majalisar nan kan yadda za a magance dambarwar da ke faruwa a yanzu?
Balarabe Musa: Da farko dai akwai bukatar ’yan majalisar su fahimci cewa sun je majalisar nan ne saboda jam’iyya, domin ita ce ta ba da sunansu ba kuma za su hau tsanin jam’iyya su hau sama ba sannan daga bisani su tozartar da jam’iyyar. Saboda hakan ba zai yi wa kasa alheri ba kuma ba zai yi wa kasa amfani ba.