NHIS: Kotu ta tsare Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje
Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje.
Kotu ta ba da umarnin tsare tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf a Gidan Yarin Kuje.
Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu ta Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja ta ba da umarnin ne bayan Hukumar Yaki da Masu Karya Tattalin Arziƙin Ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf kan zargin almundahana.
A safiyar Litinin ne EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf, inda bayan an karanta masa tuhumar da ake masa ya musanta aikata laifin.
Daga nan ne lauyansa O.I Habeeb, ya buƙaci umarnin kotu na tsare shi a ofisoshin EFCC zuwa lokacin zai shigar da buƙatar beli.
- Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da Za Mu Kashe Biliyan N2.5 Kan Auren Zawarawa —Gwamnatin Kano
Amma Mai Shari’a Chinyere Nwecheonwu, ta bayyana cewa tun da aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu, ya bar hannun EFCC.
Daga nan ta ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, 2025.
Hukumar na zargin Farfesa Usman Yusuf da bayar da kwangila ba bisa ka’ida ba da kuma almundahana a lokacin da yake shugabantar Hukumar NHIS a shekarar 2016 zuwa 2017.
Daga Nana