Dambarwar Sarautar Kano: Sarki Aminu ya nemi canjin alkali

Lauyoyinsa sun bukaci Shari’a Amina Adamu Aliyu ta fitar da kanta daga shari’ar saboda fahimtar da suka yi tana da sha’awa a shari’ar

Dambarwar Sarautar Kano: Sarki Aminu ya nemi canjin alkali

Zanen Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Lauyoyin da ke kare Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero sun nemi Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu da ta fitar da kanta daga shari’ar saboda fahimtar da suka yi tana da sha’awa a shariar.

Barista Abdurrazak Ahmad ya bayyana cewa “mun mika wa kotu wasu roke-rokenmu, daga ciki akwai neman a canza mana wani alkalin da zai ci gaba da sauraren shari’ar.

“Hujjarmu ita ce tun daga lokacin da kotun ta bayar da umarnin hakan Aminu Ado ya bayyana kansa a matsayin sarki mun san cewa kotun ta gama yanke hukunci a kan shari’ar, don haka muke ganin bai kamata kotun ta saurari wannan shari’ar ba,” in ji shi.

Sai dai a martanin masu kara ta bakin lauyansu Barista Bashir Tudun Wuzurci, ya bayyana wa kotun cewa sun riga sun mayar wa da wadanda ake kara martani a rubuce a kan wannan roko nasu.

Sai dai bangaren da ake kara sun nemi kotun ta ba su lokaci don mayar da martani ga amsar da masu kara suka ba su.

Hakan ya sa Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu ta dage sauraren shari’ar zuwa ranar  Alhamis 4 ga watan Yuli, 2024.

Masu karar dai sun hada da Kwamishinan Sharia na Jihar Kano da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Sun shigar da karar ne ta hannun lauyansu Ibrahim Isah-Wangida Esq,

Masu karar sun nemi kotu ta hana Aminu Ado Bayero da sauran sarakunan masarautu hudu da aka rushe — Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero da Dokta Ibrahim Abubakar ll, Sarkin Karaye Karaye, Alhaji Kabiru Muhammad-Inuwa, Sarkin Rano da Alhaji Aliyu Ibrahim-Gaya, Sarkin Gaya —bayyana kansu a matsayin sarakunan wadancan masarautu.

Sauran da ake kara sun hada da Shugaban ’Yan Sandan Najeriya da Daraktan Rundunar ’Yan Sandan Ciki (DSS) da Kwamandan Rundunar Sandan Sibil Difens da kuma Rundunar Sojin Kasa.

Idan za a iya tunawa a ranar 27 ga Mayu kotun ta bayar da umarni ga wadanda ake kara cewa su kansu ko yayansu ko bayinsu su daina ayyana kansu a matsayin sarakunan masarautun don samun dorewar zanan lafiya a Jihar Kano.

Aminiya ta rawaito cewa a ranar 23 ga Mayu Majalisar Dokokin Jihar Kano ta rushe dukkanin sabbin masauratun jihar guda hudu inda shi kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake nada Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano na 16