Dambarwar siyasar Kano: Kwankwaso ya janye, Ganduje ya sa kai
A ranar Litinin da ya gabata ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya janye ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa Kano a washe garin ranar, yana mai cewa an zalunce shi. Haka kuma ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun shiga siyasa har ma a yanzu kwamishinan ‘yan sandan Kano ne sabon mataimakin Gwamna Gaduje. Kwankwaso […]

A ranar Litinin da ya gabata ne Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya janye ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa Kano a washe garin ranar, yana mai cewa an zalunce shi. Haka kuma ya yi zargin cewa ‘yan sanda sun shiga siyasa har ma a yanzu kwamishinan ‘yan sandan Kano ne sabon mataimakin Gwamna Gaduje.
Kwankwaso ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ya yi da BBC a gidansa da ke Abuja, inda ya ce rashin zuwan nasa don maslahar al’umma ne ba don yana tsoron wani ba, “saboda wasu mutane sun samu kansu a madafun iko sai suke gallaza wa mutane, amma idan ba haka ba ya za a ce sanata ba zai je garinsu ba, saboda kawai an ji cewa magoya bayansa za su tare shi.”
Da aka tambaye shi ko ya ji tsoron matakin da jami’an tsaro suka dauka ne ya janye ziyarar, sai ya ce, “Dalilin janyewar tawa, saboda shugabanni ma su daraja a nan Abuja da Kano sun sa baki, sannan kuma yadda nake ganin darajar al’ummar da suka zabe mu, saboda ba na so a raunata ko a a ci mutunci ko a zubda jinin wani. Kuma a lokacin da nake ministan tsaro mun samu canji sosai game da aikin sojoji da sauran kayan damara, amma bangaren kawai da ba a samu ba shi ne ‘yan sanda. Domin sun saki layinsu sun shiga layin siyasa, ana amfani da su don a ci mutuncin mutane ba gaira ba dalili.”
“Kuma ina so ka sani, ja da baya ga rago bai zama tsoro ba. Sannan labarin da muke samu shi ne a yanzu Kwamishinan ‘yan sanda shi ne sabon mataimakin gwamna, ka ga an saki layi, amma tunda dan sanda ya shiga harkar siyasa to wata rana za mu hadu da shi”
To amma yaushe zai ziyarci Kano din an an gaba? Sai ya ce “Hakika wata rana mai zuwa zan je Kano, kuma taron da za a yi zai nunnunka wannan. Kuma ba yadda wasu za su yi don hana ziyarar faruwa, saboda masoya suna nan ba raguwa suka yi ba, karuwa ma suka yi, saboda a da wasu na kan Katanga, amma yanzu sun diro,” in ji Sanata Kwankwaso.
Tun da farko dai Sanata Kwankwason ya shirya zuwa Kano ranar Talata 30 ga watan Janairu, inda magoya bayansa suka shirya tarbarsa, amma sai kuma gwamnatin jihar ta shirya babban taro a hanyar shigar tasa.
A daya bangaren kuma, a ranar Talatar ce Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da babban taro Kwanar dangora dake karamar Hukumar kiru. Taron wanda ya dauki hankalin al’ummar jihar, kasancewar an sanya taron ne rana daya da lokacin taron da Kwankwasiyya ta yi niyyar gudanarwa a wannn rana.
Aminiya ta rawaito cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje wanda ya halarci taron, ya rarraba tutoci ga ‘ya’yan Jam’iyyar APC wadanda ke son tsayawa takarar shugabancin kananan hukumomi da kuma kansiloli a zaben kananan hukumomi mai zuwa.
Duk da cewa dubban mutane sun halarci taron, amma an takaita shi sakamakon rasuwar mahaifin Kwamishinan Raya Karkara, Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso. Bayan an kammlaa taron ne Gwamna Ganduje ya jagoranci tawagar tasa zuwa Madobi domin halartar jana’izar mahaifin Kwamshinan.
Yayin da yake wa BBC karin haske game da taron, Kwamishinna Yada Labarai na jihar Kano, Kwamared Muhamamd Garba ya bayyana taron a matsayin wanda aka gudanarwa cikin lumana a fadin jihar. “Daga abin da na gani yau, na tabbata Gwamna Ganduje zai samu nasarar zaben 2019”
Haka kuma Kwanishinan ya bayyana jin dadinsa game da dimbin jama’ar da suka fito don tarar Gwamnan Jihar a lokacin wanann taro. “Duk da surutan da aka rika yi, amma taron na Kwanar dangora ya nuna jama’ar da suka fito don tarar Gwaman Ganduje suna da dimbin yawa, sannan ya nuna cewa Jihar Kano a hannunmu take a siyasance”
Sai dai binciken Aminiya ya gano cewa an samu tashin hatsaniya a tsakanin mabiya darikar Gandujiyya a kan hanyarsu ta dawowa daga taron inda aka farfasa motocin jama’a a unguwar Na’ibawa kusa da Kwalejin Ilimi na Sa’adatu Rimi.
Har ila yau wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya bayyana cewa bayan motocin sun taho sai suka tsaya inda mutanen da ke ciki suka sassauko kamar suna tattaunawa, ba a yi aune ba sai aka ga sun fara dukan junansu tare da farfasa motocin da suke ciki. “Ba mu san abin da ya hada su ba, mu dai kawai mun ga motoci sun tsaya inda kuma bayan mutanen ciki sun fito suna maganar da ba mu san me suke cewa ba sai suka fara fada a junasu wanda ya kai ga farfasa motocinsu.Amma jami’an tsaro suka kawo dauki.’’