Dambarwar wa’adin shugabannin APC

A wannan makon ne Jam’iyyar APC ta mamaye kafafen watsa labarai game da dambarwar karewar wa’adin shugabanninta a karkashin Cif John Odigie-Oyegun. karewar wa’adin ya hada da shugabannin jihohi da kananan hukumomi a fadin kasar nan. Kuma matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka ta kasance tamkar mai da hannun agogo baya ne ga amincewar […]

Dambarwar wa’adin shugabannin APC

A wannan makon ne Jam’iyyar APC ta mamaye kafafen watsa labarai game da dambarwar karewar wa’adin shugabanninta a karkashin Cif John Odigie-Oyegun. karewar wa’adin ya hada da shugabannin jihohi da kananan hukumomi a fadin kasar nan. Kuma matakin da Shugaba Muhammadu Buhari ya dauka ta kasance tamkar mai da hannun agogo baya ne ga amincewar da Majalisar Zartarwar Jam’iyyar ta yi tun farko a  watan Feburairun da ya gabata, cewa kara wa shugabannin jam’iyyar wa’adin shekara daya a karkashin shugabancin Oyegun haramtacce ne kuma ya saba wa doka.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa gabanin ya dauki wannan matakin sai da ya yi nazari tare da duba shawarwarin da aka ba shi wadanda suka tabbatar masa da cewa an saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar. 

Ya ce, “Jam’iyyar APC ta gudanar da taron kusoshinta a ranar 27 ga  Fabrurairun da ya gabata, inda ta yi karin wa’adi ga shugabannin jam’iyyar a karkashin John Odigie-Oyegun da shekara guda. Wannan mataki ya samu amincewar mafiya rinjaye a taron da ya gabata, duk da cewa wadansu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar tamu sun nuna kin amincewarsu da daukar matakin amma aka rinjaye su.

Wadansu ma har sun riga sun dauki batun zuwa kotu. Ni kuma na dauki lokaci don sake yin tunani sannan in nemi shawara kan lamarin don yin abin da ya kamata. Amma a karshe na fahimci cewa karin wa’adin ya saba wa kundin mulkin jam’iyyar da kundin tsarin mulkin Najeriya baki daya.”

Yana mai cewa sashe na 17(1) da 13.2(B) na tsarin mulkin APC ya kayyade wa’adin shugabannin da aka zaba ne zuwa shekara hudu, wadda kawai za a iya ci gaba ne ta hanyar sake wani sabon zaben yayin da sashe na 223 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ya fayyace dukan matakan zababbun shugabannin a kowane mataki bai wuce shekara hudu. 

“Bugu da kari, jawabin kundin jam’iyyarmu ya tanadar da cewa dukan zababben da yake da burin sake tsayawa takara ko kuma ya tsaya takarar wani mukamin daban to wajibi ne ya sauka daga kan mukamin da yak e kai akalla shekara guda kafin zabe.” Sannan ya ce sake zaben shi ne mafi a’ala kuma abin da ya dace wadda kuma masu rikon kwarya ba za su iya sauya shi ba.

Wannan karfin halin da Shugaban kasa ya nuna abin yabo ne, saboda ba daidai ba ne a rika saba kowace doka da kuma kowane tsari wanda nuna cin zarafin dimokuradiyya ne. APC ta kwace mulki ne bisa doron yaki da rashin da’a da kuma rashin girmama dokokin kasa. A gaskiya ma dai batun karin wa’adin na nuni da cewa wadansu ’yan tsiraru ne da ke son yin amfani da shugabannin jam’iyyar masu barin gado, domin ba su damar cimma miyagun manufofinsu da kuma son yin amfani da damar don wulakanta abokan hamayyarsu a jihohinsu. Amma kuma sai Majalisar koli ta Jam’iyyar ta bayyana cewa an bukaci karin wa’adin ne don a magance faruwar rikici wanda zai jefa shirye-shiryen zabe cikin rudani musamman ma a jihohi inda ake samun takun-saka a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar.

Amma maimakon karin wa’adin ya kawo karshen matsalolin, sai ma ya kara hargitsa lamuran inda har wadansu ’ya’yan jam’iyyar a karkashin jagorancin Ademorin Kuye da Are Mutiu daga Jihar Legas da Sani Mayanchi daga Zamfara da  Machu Tokwat daga Kaduna suka kai jam’iyyar a kotu suna bukatar a titsiye Majalisar kolin Jam’iyyar ta yi bayanin dalilin da zai hana daukarsu a matsayin haramtattu bayan ranar 30 ga Yuni mai zuwa. Kuma sun nemi a aike da sammaci ga Hukumar Zabe ta kasa (INEC) da Jam’iyyar APC da Cif Oyegun da Babban Sakataren Tsare-tsare, Osita Izunaso.

Baya ga haka  wadansu rahotanni sun bayyana cewa jagoran Jam’iyyar APC, Sanata Bola Tinubu ya bukaci a cire shi daga shugabancin Kwamitin Sasantawar da aka nada shi don dinke barakar da ke tsakanin ’ya’yan jam’iyyar a kasar gabanin matakin Shugaban kasar da kuma dukan gwamnonin jam’iyyar suka dauka na nuna goyan baya ga sake zaben shugabannin jam’iyyar. 

Kuma ya kamata Hukumar INEC ta yi amfani da damar da take da ita wajen mai da Jam’iyyar APC cikin hayyacinta. Kamar yadda Shugaba Buhari ya hango matsalar da ke fuskantar jam’iyyar, lamarin da ya ba shi kwarin gwiwar daukar wancan matsaya a taron masu ruwa- da-tsaki na jam’iyyar, sannan gwamnoninn APC suka rufa masa baya..

Babu wata nadama cikin aikata abin da ya dace, sannan gigin mulki bai kamata ya haifar da saba doka ba. Gudanar da sahihiyar dimokuradiyya ne kawai za ta iya kai kowace jam’iyya ga gaci sannan ya dace APC ta dauki wannan batu da muhimmanci wajen fara shirye-shiyen zaben shugabannin jam’iyyar don kauce wa irin rudanin da a baya PDP ta fuskanta wadda kuma ta kawo karshen mulkinta na shekara 16 a Najeriya.