Dambe da direban Gwamna: An tsige shugaban masu rinjaye a Zamfara
’Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara sun tsige Alhaji Salisu Musa Tsafe daga Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar saboda dambacewar da suka yi da babban direban Gwamnan Jihar Malam Idris Garba a bainar jama’a kan budurwa. A ranar 4 ga Mayu ne Alhaji Salisu Tsafe da Malam Garba suka ba hammata iska kan wata budurwa da […]
’Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara sun tsige Alhaji Salisu Musa Tsafe daga Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar saboda dambacewar da suka yi da babban direban Gwamnan Jihar Malam Idris Garba a bainar jama’a kan budurwa.
A ranar 4 ga Mayu ne Alhaji Salisu Tsafe da Malam Garba suka ba hammata iska kan wata budurwa da suke nema a garin Gusau, kuma a lokacin dambacewar babban direban Gwamnan ya ciji Shugaban Masu Rinjaye a yatsunsa.
Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Zamfara Alhaji Lawali kaura ne ya kai batun gaban majalisar inda aka umarci Kwamitin da’a na Majalisar ya bincike batun fadan.
Da yake karanta sakamakon rahoton Kwamitin Alhaji Isah Abdulmumuni ya shaida wa majalisar cewa an gayyaci abokan neman matar su bayyana a gaban kwamtini tare da shaidunsu.
Ya ce kwamitin ya gano cewa dan majalisar da direban Gwamnan sun yi fada ne a kan matar da ake magana a kanta.
Kwamitin wanda ya bayyana lamarin da abin kunya bag a mutanen biyu kadai ba, ga daukacin jihar ya bayar da shawarar a tsige Alhaji Salisu Musa Tsafe daga Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar tare da dakatar da shi daga halarta ko ayyukan majalisar har zuwa karshen wa’adin zaman majalisar na wannan zango.
Kwamitin ya kuma ba da shawarar an sauya direban Gwamnan Malam Idris da wani mutum, tare da bayyana cewa daga yanzu duk wanda zai zama direban Gwamna ko mataimakinsa ko Babban Jojin Jihar da sauran manyan jami’an gwamnati a jihar wajibi ne jami’an tsaro su tantance shi domin kauce wa irin wannan abin kunya.