Damfara ta miliyan N450 aka yi rana guda —Ummi Zee-Zee
Jarumar ta yi bayanin abin da ya sa take yunkurin kashe kanta
Tsohuwar jarumar Kannywood, Ummi Ibrahim, wadda aka fi sani da Ummi Zee-Zee, ta bayyana dalilin da ya sa ta ‘yunkurin’ kashe kanta.
Ummi Zee-zee ta ce tun bayan da wani mutum dan kabilar Igbo ya damfare ta Naira miliyan 450 ta rasa me ke yi mata dadi a duniya.
- Gobara ta kashe yara 2 a Suleja
- Abin da ya sa ake binciken Masarautar Kano kan badakalar filaye
- Mahara sun kona hedikwatar ’yan sanda, sun fasa gidan yari
- Caca: Yadda N50 ta yi sanadiyyar kisan mutum 3
“Abin da ya sa na wallafa sakon shi ne akwai wani dan kabilar Igbo, dan Neja Delta, da muke kasuwancin man fetur. Ya ce akwai kasuwancin da za mu yi, zan ba da rabi daga baya na cika rabin kudin.
“Ban san cewar dan damfara ba ne, kuma na ba shi dalolin da kimarsu ta kai Naira miliyan N450, amma ya tsere da kudina. Wayarsa ko yaushe a kashe, sannan ya toshe ni a kafafen sada zumunta”, inji ta a lokacin da take karin haske kan sakon yunkurin kashe kanta da ta walla, a hirar da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya yi da ita.
Jarumar ta ce saboda dadewar da suka yi suna huldar kasuwanci da mutumin, ba ta taba tsammanin zai yi mata zamba cikin aminci ba, sai da ya bane face lokacin da ya tsere da kudinta.
“Shi ya sa na ji kamar kawai in kaske kaina saboda na ma rasa abin da zan yi.
“Yanzu na dawo Legas da zama, kuma a nan muka hadu, ban taba tsammanin haka daga wajensa ba. Abun mamaki shi ne tare da turawa suka zo waje na lokacin da za mu fara kasuwancin,” inji ta.
Zee-Zee ta ce ko gwamna ne ya yi asarar miliyan 400 dole ya girgiza, bare kuma a wajen mace ’yar kasuwa.
Kazalika, ta kara da cewa, ya zuwa yanzu ba ta sanar da jami’an tsaro faruwar lamarin ba, amma ta ba wa kanta hutun mako guda, kafin sanin matakin da za ta dauka kan lamarin.