Damina: Kada ku yi saurin shuka —AFAN ga manoma

Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Inugu Romanus Eze ya ja hankalin manoma da kada su yi gaggawar shuka saboda fara saukar ruwan sama da wuri Eze ya ce wannan ruwan ba ya jika gona har ta yi shuka, sai dai ya rage zafin iska da kuma kura. Babu wanda nake tsoro —El-Rufai ga […]

Damina: Kada ku yi saurin shuka —AFAN ga manoma

Shugaban kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Inugu Romanus Eze ya ja hankalin manoma da kada su yi gaggawar shuka saboda fara saukar ruwan sama da wuri

Eze ya ce wannan ruwan ba ya jika gona har ta yi shuka, sai dai ya rage zafin iska da kuma kura.

“Sababbin manoma na irin wannan kuskuren, amma wadanda suka dade suna yi sun san irin wannan ruwan na wuri ba ma za a kira shi damina ba.

“Don haka kada ganin yayyafi mai karfi ya sanya manoma su fara shuka, don bata lokacinsu ne da kudinsu” in ji shi.

Sojoji sun kashe kwamandan ’yan bindiga da tarwatsa 300

Zaɓen 2027: Tinubu ya sake tsayar da Shettima mataimakinsa

Tinubu ya gaji yana buƙatar ya huta — Peter Obi

Ɗalibai da malamai da aka sace a Oyo sun kuɓuta