Damun fura
Wani Bahadeje ne ya je wurin masu sayar da fura da nono, ya ce: “A ba ni gayar fura ta Naira ashirin.” Da aka ba shi sai ya sanya a baki ya cinye. Ya sake cewa: “A ba ni sukari na Naira goma.” Da aka ba shi sai ya shanye. Ya kara cewa a ba […]
Wani Bahadeje ne ya je wurin masu sayar da fura da nono, ya ce: “A ba ni gayar fura ta Naira ashirin.” Da aka ba shi sai ya sanya a baki ya cinye. Ya sake cewa: “A ba ni sukari na Naira goma.” Da aka ba shi sai ya shanye. Ya kara cewa a ba shi nono na Naira ashirin. Bayan an ba shi sai ya shanye. Yana shanyewa sai ya kama kugu yana juyawa. Aka ce masa me yake yi sai ya ce: “Dama furar nake yi!”
Daga Hajiya Loliya, 08162472249