Damun furar Bahadeje

Wani Bahadeje ne ya je wajen mai fura da nono ya ce: “A ba ni fura ta Naira 20.” Mai fura ta mika masa, shi kuwa ya karbi furar ya hadiye. Ya sake cewa: “A ba ni nono na Naira 30.” Mai fura ta mika masa, ya karbi nono ya shanye. Ya sake cewa: “A […]

Damun furar Bahadeje
Damun furar Bahadeje

Wani Bahadeje ne ya je wajen mai fura da nono ya ce: “A ba ni fura ta Naira 20.” Mai fura ta mika masa, shi kuwa ya karbi furar ya hadiye. Ya sake cewa: “A ba ni nono na Naira 30.” Mai fura ta mika masa, ya karbi nono ya shanye. Ya sake cewa: “A ba ni suga na Naira 10.” Mai fura ta sake mika masa suga, ya karbi sugar ya shanye. Bahadeje ya koma gefe ya kama kugu yana juye-juye. Mai fura ta tambaye shi ta ce: “Lafiya na ga kana juye-juye?” Sai ya ce: “Damun fura nake yi.”

Daga Hamidan Badamasi Rijiyar Lemo Kano, 07061855550