Dan ƙabilar Ibo ya zama Limamin Babban Masallacin Abuja

A yau sabon limamin Masallaci Abuja, ɗan ƙabilar Ibo, Farfesa Iliyasu Usman, zai fara jagorantar Sallar Juma’a a masallacin.

Dan ƙabilar Ibo ya zama Limamin Babban Masallacin Abuja

Masallacin Kasa da ke Abuja

A karon farko ɗan ƙabilar Ibo ya zama Babban Limami a Babban Masallacin Ƙasa da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Hukumar gudanarwar Babban Masallacin ta sanar naɗa Farfesa Iliyasu Usman ɗan asalin ƙabilar Igbo daga jihar Imo a matsayin limamin juma’a.

Da naɗin sabon limamin, yanzu limaman juma’a na masallacin sun zama huɗu ke nan, ƙarƙashin jagoranchin Babba Mai Kula da masallacin, Farfesa Ahmad Shehu Galadanchi.

Manyan Limaman su ne:

  1. Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari.
  2. Farfesa Sheikh Muhammad Kabir Adam
  3. Dakta Ahmad Onilewura
  4. Farfesa Iliyasu Usman

A yau Juma’a, 18 ga watan Oktoba, 2024 ake sa ran sabon limamin zai fara jagorantar Sallar Juma’a a masallacin.

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu