dan acaba ya kai kansa asibiti don a cire masa wukar da aka soka masa a kai

Wani dan acabar kasar Brazil ya tuka kansa zuwa asibiti da wuka tsire a kansa, inda shafe sa’o’i biyu yana ta gudu don zuwa asibiti mafi kusa, inda za a cire masa wukar, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.Juacelo Nunes dan shekara 39, yah au bisda hanya ne bayan da aka caka masa wuka […]

dan acaba ya kai kansa asibiti don a cire masa wukar da aka soka masa a kai
dan acaba ya kai kansa asibiti don a cire masa wukar da aka soka masa a kai

Wani dan acabar kasar Brazil ya tuka kansa zuwa asibiti da wuka tsire a kansa, inda shafe sa’o’i biyu yana ta gudu don zuwa asibiti mafi kusa, inda za a cire masa wukar, kamar yadda kafafen yada labarai suka ruwaito.
Juacelo Nunes dan shekara 39, yah au bisda hanya ne bayan da aka caka masa wuka ta lume a cikin kansa da kimanin tsawon inci 12. Wukar dai ta kauce bat a soki idonsa ba, inda ta makale a gefen dasashinsa, a cewar shafin sadarwar GI.
“Wukar ta lume a cikin jijiyoyinsa, kuma a wuraren da za ta iya halaka shi,” inji Likita Gilberto Albukuerkue, inda ya ce, Nunes ya fara murmurewa.
An kai masa wannan farmakin ne a garin Agua Branca, da ke da nisan kilomita 100 daga asibitin Teresina da ke Arewa maso Gabashin Jihar Piaui.
dan acaba Nunes ya yi fama da raunukan sukar wuata a makogwaronsa da kafadarsa, bayan da gardama ta kaure tsakaninsa da wani.