Dan acaba ya sace wa wata mata ‘ya’ya 3

Wani dan acaba da har yanzu hukumomi ba su ganoshi ba ya gudu da wasu yara uku ’ya’yan mace guda bayan sun je ziyara gidan kakarsu. An dai nemi yaran da babbansu ke aji hudu a makarantar firamare a kauyen Amaba Ime Oboro, a karamar hukumar Ikwuano na jihar Abiya da yammacin ranar Alhamis. Mahaifiyar […]

Dan acaba ya sace wa wata mata ‘ya’ya 3

wani yaro an rufe masa baki da hannu. (Hoto: Shutterstock)

Wani dan acaba da har yanzu hukumomi ba su ganoshi ba ya gudu da wasu yara uku ’ya’yan mace guda bayan sun je ziyara gidan kakarsu.

An dai nemi yaran da babbansu ke aji hudu a makarantar firamare a kauyen Amaba Ime Oboro, a karamar hukumar Ikwuano na jihar Abiya da yammacin ranar Alhamis.

Mahaifiyar yaran ta ce, babbansu dan shekara takwas ne, sai mai bi mishi dan shekara shida da karaminsu mai shekara hudu.

ASP Maureen Chinaka, kakakin rundunar ’yan sandan a jihar Abiya ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai ta ce har zuwa lokacin da take magana da wakilinmu mahaifiyar yaran ba ta kawo musu hotunan yaran domin zurfafa bincike ba.

Mahaifiyar yaran cikin yanayi na tashin hankali da kafuwa ta roki al’umma da gwamnatin jihar su taimaka mata wurin gano ’ya’yan nata.

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Ɗan shekara 60 ya rasu a hatsarin kwalekwale a Sakkwato

Yadda gobara ta ƙone kasuwar babura a Zamfara