dan Arewa ne zai iya magance matsalar Boko Haram – Rabaran Maina *Najeriya za ta tarwatse idan Jonathan ya lashe zabe – Malam dandada

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi Rabaran Joshua Ray Maina ya nuna damuwarsa game da yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-hare a yankin Arewa maso Gabas wanda ya yi sanadiyar lakume dimbin rayukar al’umma. Rabaran Maina ya yi kira ga matasan Musulmi da Kirista su hada kansu waje daya domin […]

dan Arewa ne zai iya magance matsalar Boko Haram – Rabaran Maina *Najeriya za ta tarwatse idan Jonathan ya lashe zabe – Malam dandada
dan Arewa ne zai iya magance matsalar Boko Haram – Rabaran Maina *Najeriya za ta tarwatse idan Jonathan ya lashe zabe – Malam dandada

Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi Rabaran Joshua Ray Maina ya nuna damuwarsa game da yadda ake ci gaba da samun karuwar hare-hare a yankin Arewa maso Gabas wanda ya yi sanadiyar lakume dimbin rayukar al’umma.

Rabaran Maina ya yi kira ga matasan Musulmi da Kirista su hada kansu waje daya domin ganin an gudanar da zabe lafiya, “domin kowa ya san ba mu da wata kasa sai Najeriya.”
Rabaran Maina ya bayyana haka ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a ofishinsa da ke Bauchi a ranar Litinin.
Ya ce, “Ina da tabbacin cewa idan dan Arewa ya zamo Shugaba kasa, to, tabbas rikicin Boko Haram zai zamo tarihi domin ’yan Arewa sun san duk hanyoyin da suka kamata a bi domin murkushe mayakan Boko Haram.
“Babbar matsalar da Shugaba Jonathan yake fuskanta a gwamnatinsa ita ce ya san halayen mutanen Kudu, amma bai san yadda zai tafiyar da ’yan Arewa ba, don haka yake fama da tarin matsaloli a gwamnatinsa.
A wani labarin kuma Babban Sakataren kungiyar Mahauta ta kasa Malam Abubakar dandada ya ce ya kamata duk wani mai kishin Najeriya ya zabi Janar Muhammadu Buhari a zabe mai zuwa domin shi ne ake da tabbacin zai iya magance mafi yawan matsalolin kasar nan.
Malam Abubakar dandada ya ce “Tun lokacin da Shugaba Jonathan ya karbi shugabanci babu abin da ya tsinana wa mutanen yankin Arewa maso Gabas saboda haka ba za mu kada masa kuri’a ba.”
Ya ce idan Jonathan ya sake lashe zabe, to, tabbas Najeriya za ta tarwatse domin kowa ya san cewa gwamnatinsa ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Sai ya shawarci al’umma da kada wani ya kuskura ya sayar da katinsa na jefa kuri’a domin da katin ne zai zabi shugaban da zai samar masa da tsaro a Najeriya.