dan Arewa zai yi takarar majalisar dokoki a Jihar Oyo

Shugaban Jam’iyar Labour bangaren ‘yan Arewa a Jihar Oyo, Alhaji Ahmad Halliru Sawaba, ya ce, zai fito takarar majalisar dokoki a mazabar Ibadan ta Arewa a zaben shekara ta 2015. Ya ce, “tarihin siyasa a wannan sashe na Kudu maso Yamma, ya nuna cewa, gwamnatocin da suka shude a Jihar Oyo, sun yi biris da […]

dan Arewa zai yi takarar majalisar dokoki a Jihar Oyo
dan Arewa zai yi takarar majalisar dokoki a Jihar Oyo

Shugaban Jam’iyar Labour bangaren ‘yan Arewa a Jihar Oyo, Alhaji Ahmad Halliru Sawaba, ya ce, zai fito takarar majalisar dokoki a mazabar Ibadan ta Arewa a zaben shekara ta 2015. Ya ce, “tarihin siyasa a wannan sashe na Kudu maso Yamma, ya nuna cewa, gwamnatocin da suka shude a Jihar Oyo, sun yi biris da al’ummar Arewacin kasa da suka shafe shekaru fiye da 100 suna zaune a wannan sashe . Wannan shi ne babban dalilin da yasa na yunkuro da dimbin magoya baya domin rungumar jam’iyar Labour, wacce muka hango cewa, ita kadai ce take da burin tafiya tare damu idan ta kafa gwamnati a zabe mai zuwa.”
 Da yake zantawa da ‘yan jarida jim kadan bayan kammala bikin bude sabuwar hedkwatar bangaren ‘yan Arewa na jam’iyar Labour a unguwar Hausawa ta Sabo a birnin Ibadan, ya ce, “muhimmin abun da ya tayar da mana da tsimi muka rungumi jam’iyar Labour, shi ne, mun hango cewa, a shekarun baya a duk lokacin da aka fara batun siyasa sai ka ga mafi yawancin al’ummar Arewacin kasa ‘yan siyasa da ke zaune a wannan sashe sun karkatar da akalarsu ga jam’iyya daya tak, wanda yin hakan ya sa ake tafiya ba tare damu ba. Wannan yana janyo mana babbar illa ga ci gaban mu. Da yawa daga cikin gwamnatcin jihohin Arewa, sun janyo bakin kabilu na Yarbawa da Ibo suna tafiya tare da su a harkokin mulki, amma abun ba haka yake ba a wannan sashe.”
 Alhaji Ahmad Halliru Sawaba, ya kawo misali da Gwamnatin Jihar Ondo da ke mulki a karkashin tutar jam’iyar Labour wacce ta janyo mutanenmu a jiki ta ba su mukaman siyasa da rancen miliyoyin kudi ga kungiyoyin ‘yan kasuwa ‘yan Arewa, domin bunkasa harkokin kasuwancinsu a jihar. “Irin haka muke bukatar  samu a Jihar Oyo da sauran jihohin yamma, shi ne dalilin da ya kaimu ga ficewa daga jam’iyyu daban-daban muka rungumi jam’iyar Labour domin samun mafita. Abun mamaki shi ne, akwai daruruwan yaranmu da suka kammala karatun digiri na farko zuwa na uku a manyan makarantu da jami’o’i, amma ba sa samun guraben ayyuka sai sun koma jihohinsu na asali a Arewacin kasa. Shi ne yasa muka fito domin fafutukar  neman sauyi. ‘Yancinmu yana hannunmu. Ba za mu taba amincewa da siyasar yaudara da ake amfani da kudi wajen neman kuri’unmu a lokutan zabe ba.”
Dangane da sha’awar  tsayawa takarar kujerar majalisar dokoki ta jihar oyo da yake yi, sai ya kada baki ya ce, “wannan shi ne karo na farko da wani dan Arewacin kasa mazaunin Jihar oyo, ya nuna sha’awarshi ga wannan kujera kuma mun kammala shirye shirye da hadin guiwar uwar jam’iya a kan hakan. Mun cancanci neman wannan matsayi wanda dokar kasa ta amince da hakan. Shi ne yasa muka fito domin neman goyon bayan mutanenmu. Har mun fara zagayawa zuwa manya da kananan garuruwa a jihar oyo domin wayar da kan mutanenmu a kan amfanin dake tattare da jam’iyar Labour da muke fatan za mu samu hadin kai da goyon bayan jama’armu idan lokacin yakin neman zade ya iso su kada kuri’unsu ga ‘yan takarar jam’iyar Labour.”
Shugaban Jam’iyar Labour a Jihar Oyo, Hon. Gbenga Olayemi, shi ne ya jagoranci wasu kusoshin jam’iyar da suka hada da tsohon Sakataren Gwamnatin jihar, SSG Alhaji Sarafadeen Ali da tsohon Kwamishinan tsaftace muhalli Barrister Lowo Obisesan zuwa wajen bikin bude sabuwar hedkwatar jam’iyar Labour, bangaren ‘yan Arewa.