dan ba a Gwamnatin Masari (4)
Idan kuma muka yi nazarin yadda matsalar rashin isasshen ruwan sha take kwance a cikin birnin Katsina kurum, sai mutum ya ci gaba da yin tagumi, domin kuwa a lokacin mulkin Gwamna Shema, an ce an kashe sama da Naira miliyan 826 domin tabbatar da samuwar ruwan famfo a cikin birnin Katsina. Haka an kashe […]
Idan kuma muka yi nazarin yadda matsalar rashin isasshen ruwan sha take kwance a cikin birnin Katsina kurum, sai mutum ya ci gaba da yin tagumi, domin kuwa a lokacin mulkin Gwamna Shema, an ce an kashe sama da Naira miliyan 826 domin tabbatar da samuwar ruwan famfo a cikin birnin Katsina. Haka an kashe sama da Naiar miliyan 63 domin inganta harkar ruwan famfo a wasu manyan garuruwan jihar ta Katsina. Haka an zuba sama da Naira miliyan 80 domin inganta hanyar rarraba ruwan sha da ke Masabo. Baya ga wadannan kuma an ce an sayo injinun yin rijiyoyin bohol ko na burtsatse na kusan Naira miliyan 337. Idan har an kashe wadannan makudan kudi tun da dadewa, to ina matsalar take? Me ya sa ba isasshen ruwan famfo a Katsina? Me ya sa a Funtuwa ake kukan rashin ruwan famfo? Me ya sa Malumfashi ake ta ganin tankunan motocin ruwa na yawo domin rarraba ruwa? Me ya sa Daura ake ta kamfar ruwan famfo? Me ya sa ba a jin duriyar ruwan famfon a Mani ko Kankiya ko Dutsinma ko Jibiya? Idan har wadannan manyan garuruwa suna fuskatar karancin ruwan sha, to, me muke tsammani yake faruwa a Kuka-Sheka ko Makauraci ko Mai’aduwa ko Mashi ko Batsari ko Maska ko wani kauyen da kila idan suna bukatar ruwan sha sai dai su bi dabbobinsu, idan sun sha, su kuma su debo na sha da na dafa abinci? Nan ma fa ana maganar wadanda Allah Ya tofa wa garinsu nono ke nan, wato suna da tafki ko korama ko wani rafi a kusa da su; domin wasu sai sun yi tafiya mai nisa kafin su samo tarfi!
Saboda haka za mu iya cewa ana bukatar sake nazari game da tasoshin samar da ruwan famfo guda shida da ke a garuruwan Katsina da Funtuwa da Malumfashi da Daura da Dutsinma da Jibiya domin yi wa tufkar hanci. Da alama nan ne farkon matsalar, wadda kuma ina tsamanin Mai girma Gwamna ya san da haka!
Abin da kurum zan kara shi ne wadanda ke kula da wadannan tasoshi su kansu su damu da halin da ake ciki, gwamnati ce kurum ke yin kunnen-uwar-shegu. Alal misali a wata hira da aka taba yi da wani Manajan Tashar samar da ruwa da ke Jibiya, Alhaji Rabe Musa ya nuna cewa babbar matsalar tashar ita ce ta rashin wutar lantarki, a lokutta da dama suna samun dauki ne daga Shugaban karamar Hukumar Jibiya, wanda duk wata ke ba su kudin sayen dizal domin ta da injinun samar da ruwan famfon. Ya kara da cewa duk lokacin da ba su samu wannan dauki ba, to ba sa iya samar da ruwan famfo, in ba NEPA ta kawo wuta ba! Ka ga a nan an ga wata, rashin makamashi ne!
Haka ma matsalar take a Dutsinma. Bincike ya nuna cewa a lokutta da dama karamar Hukumar Dutsinma ce ke samar kudin dizal domin a ta da injinan ruwa a Dutsinma, musamman a zamanin Gwamna Ibrahim Shema, tun da yankinsa ne. Idan ba ruwa a Dutsinma to ai Gwamna Shema ya ji kunya, musamman in Gwamna da bakinsa na gari. Duk da cewa hakan na iya zama gaskiya, sai na ga cewa wannan tunanin ba dalili ba ne, wane Gwamna ne ko Kwamishina ko Kansila ke damuwa da ruwan gwamnati, duk bohol gare su na kansu, ke nan ko a samar da ruwan famfo ko kada a samar, shakulatin bangaro…! Haka wannan batu yake a Malumfashi da Daura da sauran wurare. Ke nan talakawa ne kawai ke cikin tasku. Me za mu iya yi domin maganin wannan a zamani na canji? Akwai abubuwa da dama, na san kuma Gwama Masari ya san da wasu, sai dai mu yi tuni.
Mu fara da neman bayani. Tambayar da zan fara da ita ita ce, shin wai ba a iya maganin wannan matsala ta rashin ingantaccen ruwan sha ne ko kuwa dai akwai wata manufa ce ta daban, ya Mai girma? Ina ga ba maganin matsalar ce babu ba, ba kuma don ba a iyawa ba, sai dai rashin mai da hankali a yi hakan ne ba za a yi ba. Wannan ya kasance haka ne ganin cewa duk shekara ta Allah sai an tanadi makudan kudi domin a tada komadar samar da ruwan famfo a Jihar Katsina, amma kamar yadda aka sha fada, abin tamkar ana mai da ruwa cikin rijiya ne. Ba wannan kadai ba, ya Mai girma hatta Gwamnatin Tarayya da ta kawo dauki kan wannan lamari da fatar a ga cewa an samar da dam-dam da za a yi amfani da su domin noman rani daga nan kuma a shiga harkar samar da ruwan sha domin al’ummar Jihar Katsina, nan ma ba ta sake zane ba, domin duk da an kashe makudan kudi wajen gina wasu daga cikin dam-dam din, har yau ba a ci gajiyarsu ba, ko dai ta hanyar noman ranin ko kuma uwa-uba ta samar da tsabtataccen ruwan sha, nan kuma me za mu iya yi don kawo sauki, ba wai ta fatar baki ba, ta hanyar dabashiri da aikatawa!
Bari in dauki Mai Girma zuwa cikin tarihi mu ga in za mu iya nuna inda aka taso da inda ake a halin yanzu dangane da wadannan dam-dam da ke tsugune a cikin Jihar Katsina. Na san Mai girma ya san muhimmanci tarihi a harkar gina ci gaban al’umma, kuma na saurare shi a lokacin tattaunawa da ya yi da dattawan Jihar Katsina game da dam na Zobe da tunaninsa kan yadda za mu iya cin moriyarsa. Abin da na ji, ba shi na so na ji ba. Ga nawa tunanin.
Mu koma kan dam din Zobe, bincike ya nuna cewa an assasa wannan dam ne tun a shekarun 1970, zamanin mulkin Janar Obasanjo, an kuma kudurta idan an kammala shi zai iya samar da tsabtataccen ruwan sha da kashi 50 cikin 100 na al’ummar Jihar Katsina, ba wai karamar Hukumar Dutsinma ko makwabta kurum ba. Ka ga ke nan tunanin Mai girma ya wuce na jan ruwan daga Zobe zuwa Katsina kawai, kashi hamsin na al’ummar jihar za a dinga sa wa a dabashirin gwamnati, har Allah Ya sa mu kai tudun mun-tsira. Me za a iya yi domin cimma wannan manufa, shi ma zama za a yi a bata hankalin dare don neman mafita, ba surutu irin na kamfen ba, tun da an ci zabe!
Na fadi haka ne domin ganin har yau ba ta canza zane ba tun daga1983 dangane da wannan dam. A lokacin mulkin Shehu Shagari an ce ruwan sha zai fara malala daga dam na Zobe daga 1995. Aka canza rana da lokaci zuwa shekarar 2003, sai ga shi kududdufan da aka tanada na tsawon kilomita kusan biyu da rabi ba a ma kammala su ba, duk kuwa da cewa an assasa tasoshin aika ruwa da tankunan ajiye ruwan a bisa titin da ya tashi daga Zobe zuwa Katsina. Ya Mai girma, gwamnati bayan gwamnati, tunda aka fara aikin dam na Zobe aikin ke nan, a fara a tsaya, wato dai gutsiri-tsoma.
Mu tuna cewa ko Gwamna Umaru Musa ’Yar’aduwa sai da ya yi kamar da gaske a shekarar 2003, inda ya zuba Naira miliyan 317 domin ya ga ko zai iya sa a yi amfani da dam din na Zobe don samar da ruwan sha a garin Dutsinma, in ba za a iya kai shi har cikin birnin Katsina da makwabta ko rabin fadin jihar ba kamar yadda aka tanada, amma me ya faru, abin da aka saba ji da gani ne. Tsit!
Za mu ci gaba