dan Ba Ga Gwamnatin Masari (5)

Dukkan bayanan da muka kawo game da dam na Zobe, kila abin haka yake da sauran dam-dam da ke baje a cikin jihar Katsina, wadanda za a iya amfani da su domin samar da ruwan sha ga al’mmar Jihar Katsinan. Mu waiwayi dam din Jibiya da ke cikin jihar Katsina shi ma. An yi shekaru […]

dan Ba Ga Gwamnatin Masari (5)
dan Ba Ga Gwamnatin Masari (5)

Dukkan bayanan da muka kawo game da dam na Zobe, kila abin haka yake da sauran dam-dam da ke baje a cikin jihar Katsina, wadanda za a iya amfani da su domin samar da ruwan sha ga al’mmar Jihar Katsinan. Mu waiwayi dam din Jibiya da ke cikin jihar Katsina shi ma. An yi shekaru ana ta cece-ku-ce da wannan aiki na dam din Jibiya. Dam din kamar kowane an tsara shi ne ya samar da wurin noman rani da ruwan sha ga al’ummar jihar, an kuma ba da kwangilarsa tun a shekarar 1986, aka soma cin moriyar wani sashe nasa a 1992. Shi ma an tanadi kududdufai na tsawon kilomitoci masu yawa don ajiye ruwa duk daminar Allah. Ta haka aka tsara shi yadda zai samar da ruwan sha isasshen ga al’ummar Jibiya da makwabta. Duk da cewa an kammala wani bangare na dam din, kuma ana samar da ruwan sha, amma ba kullum ba, ba kuma ko’ina ke samun wannan dama ba ko a can garin Jibiyan. Matsalar nan ma kuma ta rashin makamashin wutar lantarki ne. Bincike ya nuna cewa idan dai ka ga ruwan famfo na tsiyaya a cikin garin Jibiya to akwai wutar NEPA, idan an dauke kuwa, tun da ba a iya sayen disil sai dai ‘yan-ga-ruwa su sha romonsu. Saboda haka matsalar ruwan sha a garin Jibiya da makwabta ba ta wuce ta rashin kudin da za a sayi disil ba in ba wutar lantarki, ke nan dam din kusan kalau yake, aljihun gwamnati ne ke fama da fatara, saboda haka kishirwa sai dai ta kashe al’umma in ba an kawo dauki ba.

Idan kuma muka koma kan madatsar ruwa ta Sabke da ke karamar Hukumar Mai’adua a kasar Daura, sai a ga cewa nan ma ba ta canza zane ba. Shi dai wannan dam daga dan binciken da na yi, an gina shi ne tun zamanin da Janar Buhari ke shugaban hukumar PTF. Ba sai an nanata ba, duk wani aiki da wannan hukuma ta yi ko ta ayyana yi karkashin Janar Buhari, aiki ne mai alfanu ba wai ga wadanda suka rayu da aikin ba har ‘ya’ya da jikoki, Saboda haka an assasa wannan dam da manufa biyu, a samar da wadataccen ruwa da zai taimaka wajen noman rani da kuma samar da tsaftataccen ruwan sha ga al’umma.
Shi ma wannan aiki duk da cewa an kammala kusan kashi 80 cikin 100, amma al’ummar Daura ko jihar ta Katsina ba ta fara more masa sosai ba har yanzu. Tun lokacin da aka fara aikin a zamanin na PTF an kashe masa sama da naira bilyan biyu, daga baya aka yi watsi da aikin, musamman a zamanin mulkin Obasanjo, da marigayi ‘Yar’adua ya hau aka ci gaba aiki, musamman bangaren da ya shafi noman rani, an kuma kammala, abin da ya rage shi ne kamfanin CGC da ya yi aikin da ya ki ya saki ruwa zuwa rafukkan da aka tanada don ajiye ruwan. Kamar yadda bincike ya nuna, kamfanin CGC na bin Gwamnatin Tarayya a lokacin wasu daga kudin kwangilar da aka amince za a ba shi, don haka ya boye makullan sakin ruwan sai an biya shi!
Saboda haka madatsar ruwan ta Sabke ta kasance tamkar ya babu, domin kuwa ta kasa samar da ruwa domin noman rani, sannan ta kasa samar da ruwan sha ga al’ummar yankin Daura da makwabta. Ba kuma wai don ba ruwan tattare a madatsar ba, sai don kawai ko-in-kula da Gwamnatin Tarayya ta yi da wannan aikin da ba kowa zai amfanar ba, in ba al’ummar jihar Katsina ba.
{ila abin da wani zai iya cewa ai wannnan ba laifin gwamnatin jihar Katsina ba ne, kuma ba ruwan Gwamna Masari da wannan badakalar tun da kuwa ya gabaci gwamnatinsa. Eh haka ne, amma kuma in aka natsu za a fahimci cewa ba hakan ba ne. Wasu za su ita cewa ai ba lokacin gwamnatin Masari aka assasa wannan aiki ba, ba kuma gwamnatin jihar ke da hurumin gudanar da shi ba, don haka sai a yi kunnen uwar shegu da abin da zai iya amfanar al’ummar jihar Katsina?
Ba wannan ba ma kadai, ai madatsar ruwa ta Zobe da wadda ke Jibiya kamar na Sabke ne, duk shiri da tsarin Gwamnatin Tarayya ne, amma wannan bai hana Gwamnatin Jihar ta sa hannu a cikinsa ba. Mun ga yadda marigayi Gwamna ‘Yar’adua ya sa hannu da kudin jihar Katsina domin kammala wani sashe na samar da ruwa a dam na Zobe domin a ga ko zai wadatar da al’ummar Dutsinma kurum, ba kuma wanda ya ce da shi ahir! Haka kuma mun ga yadda gwamnatin Gwamna Shema ta nemi Gwamnatin Tarayya ta amince mata ta ida wani bangare da ya shafi noman rani, ganin cewa sama da shekara 20 da fara aikin an kasa kai gaci, Gwamnatin Tarayya ta amince, gwamnatin Shema ta yi ruwa ta yi tsaki wajen gyara da inganta wani bangare na dam din Jibiya don amfanin al’ummar jihar Katsina.
Idan har za a iya kashe makudai daga dukiyar talakawa don a inganta rayuwarsu ta hanyar noman rani ke nan za a iya kashe wasu makudan domin samar da ruwan sha daga irin wannan tsari. Idan kuma Gwamnatin Masari ta sa fuska kan wannan batu, ba karamar gudunmuwa za ta bayar ba wajen raya al’ummar jihar ta fuskar samar da ruwan sha.
Kamar kuma yadda muka sha fada tun daga lokacin da muka faro wannan sharhi, matsalar ba ta rashin kudi ba ce, in ma akwai maganar rashin kudi, to me za a iya yi a samar da kudaden don tabbatar da cewa ruwa abokin aiki ya dawwama a karkara da garuruwa da biranen jihar Katsina? Yin haka taimako ne na kin karawa!
A lura da wata hikima da gwamnatin Tarayya ta yi wa al’ummar jihar Katsina; babbar madatsar ruwa a Jibiya, wata a Dutsinma, wata a Daura! Idan za a kyautata da inganta ayyukan samar da ruwan sha daga wadannan madatsu me ake tsammanin zai faru? Ruwan sha zai malala, ciki da wajen jihar Katsina. Dam din Sabke ya shayar da Daura da yankinta, na Jibiya ya shayar da Jibiya da Katsina da yankinsu, na Zobe a mazaya da shi ya nufi Malumfashi da Funtua da yankinsu. Ga kuma na Ajiwa nan rakube idan abubuwa sun rincabe daga baya da ma wadansu kananan dam da ke warwatse a cikin jihar baki daya.
Idan da Masari da gwamnatinsa za su dubi wannan batu da ma wadansu da ban tabo ba da idon rahama, su kuma tabbata sun yi abin da ya dace, na tabbata har Mahdi ba za a taba mantawa da su ba.
Saura da me ni dai na zazzage abin da ke kimshe a cikin raina. Fatata ita ce wannan sharhi ya zunguro abin da ke zunguruwa ya kuma tayar mana da kaimi bisa ga son inganta rayuwar al’ummar da ke bukatar taimako daga mu ‘yan jihar da kuma gwamnatinmu.

An Kammala