dan banga ya bindige abokinsa a wurin bikin nadi

Wani dan banga a garin Damaturu da ke Jihar Yobe ya bindige abokin aikinsa sakamakon kwacewar harsashi a lokacin bikin murnar nada musu sabon Sarkin Bakan Yadin Buni da ke jihar.Wannan lamari ya faru ne a ranar Jumu’ar da ta gabata a kofar gidan Mai martaba Mai Gujba Alhaji Mukhtar Ibn Ali Gangaran da ke […]

dan banga ya bindige abokinsa a wurin bikin nadi
dan banga ya bindige abokinsa a wurin bikin nadi

Wani dan banga a garin Damaturu da ke Jihar Yobe ya bindige abokin aikinsa sakamakon kwacewar harsashi a lokacin bikin murnar nada musu sabon Sarkin Bakan Yadin Buni da ke jihar.
Wannan lamari ya faru ne a ranar Jumu’ar da ta gabata a kofar gidan Mai martaba Mai Gujba Alhaji Mukhtar Ibn Ali Gangaran da ke cikin garin Damaturu jim kadan bayan Sarkin ya nada Sarkin Maharban masarautarsa da ake kira da Sarkin Baka Bukar Soja Buni Yadi.
Wani ganau a cikin ’yan bangar da ya nemi a boye sunansa ya bayyana wa Aminiya cewa yadda lamarin ya faru shi ne shi dan bakan da harsashin bindigarsa ya kwace ya samu dan uwansa bayan da aka nada sabon Sarkin Baka kamar yadda al’ada take, sai suka shiga harba bindiga sama don nuna murnarsu.
Ya ce, bayan da abokin aikin nasu ya yi kokarin harba bindigarsa sama ne sai ta ki tashi, kuma a kokarinsa na ya sauke ta don duba me ya hana ta tashi ne sai kawai ta tashi gab da ya
sunkuyo kanta gab da marigayin shi ne harsashin ya same shi har ya zama ajalinsa.
Ya kara da cewa, nan da nan suka sanar da ofishin ’yan sandan A. Dibision da ke kula da yankin tare da daukar marigayin zuwa babban asibitin Damaturu don duba shi.
Aminiya ta tuntubi sabon Sarkin Bakan Bukar Soja ta waya dangane da faruwar lamari, inda ya ce, lallai hakan ya faru bisa ga tsautsayi, kuma hankalinsa ya yi matukar tashi kan hakan. Sai dai ya ce babu abin da zai ce tunda lamarin na hannun ’yan sanda suna binciken kan yadda lamarin ya faru.