Dan bindiga ya tona ’yan siyasar da ke daukar nauyinsu
Dan bindigar da aka kama ya ce wasu manyan ’yan siyasa ne suka sa shi a harkar.
Wani dan bindiga da ya shiga hannu a Jihar Sakkwato ya fallasa iyayen gidansu a cikin manyan ’yan siyasa.
Kwamandan Hukumar Tsaro ta Sibil Difens (NSCDC) na Jihar Sakkwato, Saleh Dada, ya tabbatar wa Kamfanin Daillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa dan bindigar mai suna Danlabbo ya shaida musu cewa shi makusancin wasu manyan ’yan siyasa ne kuma su ne suka sanya shi a harkar ’yan bindiga.
- Buhari ya bullo da shirin noma na ‘ciyar da kanka’
- Harin ’yan bindiga: Sojoji na bukatar N500m don katange NDA
Danlabbo ya yi wannan fallasa ne bayan Hukumar ta kama shi da wasu ’yan bindiga da masu kai musu bayanai hudu a yankunan jihohin Sakkwato da Zamfara.
Kwamandan ya ce tuni suka fara gayyato dan siyasan da Danlabbo ya ambaci sunansa domin amsa tambayoyi a ofishin hukumar. Sai dai bai bayyana wa majiyarmu sunan dan siyasar ba.
Da yake gabatar da su a ranar Laraba, Kwamandan hukumar ya ce daya daga cikin ’yan bindigar da dubunsu ta cika kuma ya tabbatar musu cewa ya kashe mutane da dama a hare-haren da suka kai.
Sun kuma tabbatar wa hukumar cewa da su ake yin garkuwa da wasu manyan mutane, satar dabbobi da kashe-kashe da sauran ayyukan ta’addanci a kauyukan jihohin Sakkwato da Zamfara.
Ya ce mutanen da aka kama ’yan asalin yankunan Tureta da Dange-Shuni ne a Jihar Sakkwato, kuma shekarunsu 27 ne zuwa 48.
Hukumar ta kuma kama wani mutum mai shekara 35 wanda ake zargi ya lalata kananan almajirai 12 ta hanyar zakke musu ta dubura.