Dan bindiga ya kashe sama da mutane 50 a Amurka
Wani dan bindiga ya kashe sama da mutane 50 sannan wasu kimanin 200 suka jikkata bayan wani hari da ya kai a wani gidan rawa a birnin Las Vegas da ke kasar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata. Wannan harin shi ne hari ma fi muni a tarihin Amurka na tsawon lokaci, kamar yadda […]

Wani dan bindiga ya kashe sama da mutane 50 sannan wasu kimanin 200 suka jikkata bayan wani hari da ya kai a wani gidan rawa a birnin Las Vegas da ke kasar Amurka a ranar Lahadin da ta gabata.
Maharin ya fara bude wuta ne daga hawa na 32 na benen wani otel mai suna, Mandalay Bay Hotel, inda ya hari wani wuri da ake wasan raye-raye.
Daruruwan mutane sun tsere daga wurin kuma an rika jin karar harbe-harbe a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
‘Dan Sandan Las Vegas da ke sintiri a birnin na Las Vegas yana cikin wadanda suka rasa rayukansu a harin.