Dan bindigan da ya kai wa ’yan sanda hari ya shiga hannu
Mahara sun kai farmaki kan ’yan sandan da ke sintirin samar da tsaro a garin Benin
Rundunar ’yan sanda ta yi nasarar kama wani mutum da ake zargi da kai wa jami’anta harin bindiga a Benin, baban birnin Jihar Edo.
An kai wa ’yan sandan hari ne a yayin da suke sintiri a Benin domin hana masu aikata munanan ayyuka.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya ce ’yan bindigar sun kai wa jami’an sashin Ugbekun hari ne a kan hanyar Nomayo, a cikin garin.
Ya ce daya daga cikin ’yan ta’addan ya samu rauni a yayin musayar wuta da jami’an nas a harin na ranar Litinin.
- An kama mai garkuwa da mutane a Kogi
- NAJERIYA A YAU: “Tabbas Muna Biyan Ma’aikatan Borno Albashin N7,000”
Wanda aka kama bayan ya ji raunin ya amsa cewa yana daga cikin waɗanda suka kaiwa ’yan sandan hari.
Kwamishinan ya ce an kwaci wata bindiga ƙirar gida da harsaai biyu daga hannun wanda ake zargin.