Dan Brazil ya ba da wasiyyar kyautar da dukiyarsa ga Neymar idan ya mutu

Matashin ya ce ba ya son gwamnati ko danginsa su ci gadonsa

Dan Brazil ya ba da wasiyyar kyautar da dukiyarsa ga Neymar idan ya mutu

Neymar

Ba kowa ne dai zai iya cewa idan ya mutu, duk abin da ya mallaka a ba wani attajirin dan kwallo ba, amma wani masoyin dan kwallon kafa ya aikata haka.

Mutumin, wanda ba a bayyana sunansa ba dai ya zabi mallaka duk dukiyarsa ga dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG kuma dan asalin kasar Brazil, wato Neymar.

A cewarsa, ya yi hakan ne saboda tsananin kishin da dan wasan yake da ita ga tawagar kasarsu ta Brazil.

Ya ce, “Ina son Neymar, abubuwansa da dama suna birge ni. Amma a kan haka, na sha fama da tsangwama iri-iri. Alakar Neymar da mahaifinsa tana tuna min nawa mahaifin ni ma matuka.

“Ba ni da cikakkiyar lafiya, a saboda haka, na ga ba ni da wanda zai ci gadona idan na mutu, ba na son gwamnati ko ’yan uwana su ci gadona,” in ji shi.

Matashin mai shekara 30 ya ce tun a baya ya sha yin kokarin mallaka wa Neymar din dukiyar tasa, amma bai yi nasara ba.

Ya ce amma a yanzu ya bi dukkan matakan da doka ta tanada wajen bayar da wasiyyar, kuma an rattaba hannu a kan yarjejeniyar ce a ofishin da ke kula da wasiyyar na birnin Port Allegre.

Neymar dai na daya daga cikin ’yan wasan da suka fi daukar albashi a jerin ’yan kwallon kafa a duniya, inda mujallar Forbes ta yi hasashen zai samu Dalar Amurka miliyan 85 a bana.

Manyan alhinin Najeriya a 2024

’Yan sanda sun kama waɗanda suka shirya rikicin ‘yan daba a Kano

Ɗan Gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

Mutum 38 ne suka mutu a haɗarin jirgin sama a Kazakhstan

Tags