dan Brazil ya mutu a lokacin da yake kallon bugun fanariti

Wani tsoho dan kimanin shekara 69 mai goyon bayan kasar Brazil a gasar cin kofin duniya ya samu matsalar bugun zuciya da hakan ta yi sanadiyyar mutuwarsa a lokacin da yake kallon bugun fanariti a tsakanin kasar da ta Chile a karshen makon jiya.Tsohon wanda ya shiga filin wasa na Mineirao mai cin mutum dubu […]

dan Brazil ya mutu a lokacin da yake kallon bugun fanariti
dan Brazil ya mutu a lokacin da yake kallon bugun fanariti

Wani tsoho dan kimanin shekara 69 mai goyon bayan kasar Brazil a gasar cin kofin duniya ya samu matsalar bugun zuciya da hakan ta yi sanadiyyar mutuwarsa a lokacin da yake kallon bugun fanariti a tsakanin kasar da ta Chile a karshen makon jiya.
Tsohon wanda ya shiga filin wasa na Mineirao mai cin mutum dubu 62 da ke garin Belo Horizonte ne don ya kalli yadda zai kaya wasa a tsakanin kasarsa da ta Chile ya samu matsala ne jim kadan bayan an tashi wasan da ci 1-1.&nbsp Duk da mintuna 30 da alkalin wasa ya kara wasan bai kaya ba sai a bugun&nbsp fanariti.
Ana gab da fara bugun fanaritin ne sai aka ga tsohon ya fara rawar sanyi kuma ya shaida wa wadanda ke kusa da shi ba ya jin dadi al’amarin da ta sa aka garzaya da shi asibiti mafi kusa.&nbsp Jim kadan da isa asibitin ne rai ya yi halinsa
Kamar yadda jaridar Estado ta kasar ta ruwaito tsohon yana daga cikin mutane 98&nbsp da suka samu matsala a lokuta daban-daban&nbsp daga lokacin da gasar ta fara kawo yanzu.
Rahoton ya ce akalla mutum 60 ne likitocin da ke zaga filin kwallon don bayar da taimakon gaggawa suka ceto rayuwarsu a matsalolin da suka shafi bugun zuciya da na hawan jini a lokuta daban-daban daga fara gasar kawo yanzu.
A bugun fanaritin da aka yi Brazil ce&nbsp